Rundunar ’yansandan jihar Sokoto ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a mallaka da hada-hadar jabun kuɗi a sassan jihar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, rundunar ta kuma kwato bindiga kirar AK-47 da tumaki 180 a wasu samame daban-daban da jami’anta suka kai.
Mai magana da yawun rundunar ’yansandan jihar, Ahmad Rufa’i, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Ya ce jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane sun gano wata ƙungiya da ake zargi da yin jabun kuɗi wadda ake kira “Sai Malam.”
A cewarsa, jami’in ’yan sanda na sashen Illela ya kama wasu mutane uku da ake zargi, sannan aka tura su sashen binciken manyan laifuka domin ci gaba da bincike.






