Home Labarai Wa da ƙanin sa sun rasu a ruwa yayin da ƴan ƙwacen...

Wa da ƙanin sa sun rasu a ruwa yayin da ƴan ƙwacen waya ke ƙoƙarin kai musu hari a Kano

8
0

Wasu matasa, ƴan ɗaki ɗaya, Sadiq Isyaku da Auwalu Isyaku sun rasu a wani kudiddifi a unguwar Kureken Sani a jihar Kano.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kwana-kwana ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata a jihar Kano.

Ya ce lamarin ya faru a ranar Juma’a bayan da rundunar ta karbi kiran gaggawa daga wani Muhammad Abba cewa yaran su biyu sun fada ruwa.

Ya ce da jami’an hukumar suka garzaya wajen sai su ka yi kokarin ceto yaran, inda aka fito da su ba da motsi, daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwar su.

Abdullahi ya ce tuni aka mika gawarwakin matasan zuwa ga mahaifin su a Unguwa Uku.

A cewar Abdullahi, binciken farko da hukumar ta gudanar ya nuna cewa yaran sun fada ruwan ne domin tsira daga ƴan ƙwacen waya da su.ke bin su da su yi musu kwace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here