Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris (Kauran Gwandu), ya bayar da umarnin a gaggauta kafa wani kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin gobarar da ta tashi a Makarantar Nurul Haqq Qur’anic and Arabic School da ke Birnin Kebbi.
Lamarin, wanda ya faru a yammacin ranar Asabar, ya shafi dakunan kwanan ɗalibai da azuzuwa da dama a harabar makarantar. Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne jim kaɗan bayan ya jagoranci sa ido kan matakan gaggawa da aka ɗauka a wurin da abin ya faru.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Yahaya Sarki, Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, wadda aka fitar a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.
Gwamnan, wanda ke kan hanyarsa ta zuwa buda baki, ya hango hayaƙi mai yawa yana tashi a gefen hanya, inda nan take ya umarci ayarinsa su tsaya domin gano tushen hayaƙin.
Da aka tabbatar cewa daga harabar makarantar hayaƙin ke fitowa, sai ya bayar da umarnin fitar da ɗalibai gaba ɗaya tare da kiran Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kebbi da sauran jami’an agajin gaggawa domin shawo kan lamarin.
Duk da cewa ana gab da shan ruwa, Gwamnan ya jajirce tare da tsayawa a wurin domin tabbatar da cewa an kubutar da dukkan ɗaliban da ke cikin makarantar. Ya ci gaba da kasancewa a wurin har sai da ya tabbatar an kashe gobarar gaba ɗaya.
Gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, tare da gode wa Allah Maɗaukakin Sarki da babu asarar rai.
Haka kuma, ya yaba wa Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kebbi bisa saurin amsa kiran gaggawa, ƙwarewa da jajircewa wajen tafiyar da aikin yadda ya kamata.
Gwamna Idris ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da lafiyar ɗalibai a faɗin Jihar Kebbi, yana mai cewa kwamitin binciken zai zurfafa wajen gano asalin matsalar tare da bayar da shawarwarin da suka dace domin kauce wa sake faruwar irin wannan lamari a makarantu a faɗin jihar.
DAGA: Ibrahim Abubakar.





