Home Siyasa Sanata Lamiɗo ya ƙaddamar da sabbin shugabannin APC na ƙananan hukumomi 23...

Sanata Lamiɗo ya ƙaddamar da sabbin shugabannin APC na ƙananan hukumomi 23 a  Sakkwato 

4
0

Sanata Lamiɗo ya ƙaddamar da sabbin shugabannin APC na ƙananan hukumomi 23 a  Sakkwato 

Sanata Ibrahim Lamiɗo ya ƙaddamar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi 23 na APC da aka zaɓa a satin da ya gabata.

Sanata Lamiɗo a lokacin da yake ƙaddamar da shugabannin a birnin jiha ya taya su murna tare da neman su yi aiki tuƙuru domin samun nasarar APC a jiha da ƙasa baki ɗaya.

Ya ce uwar jam’iya ta ƙasa ta  amince da a yi zaɓen shugabannin ta hanyar sasanci ko zaɓe daga waƙillan jam’iya, in da muka fitar da shugabanni a Sakkwato ta hanyar sasanci.

Sanata bayan ya bayyana Honarabul Kabiru Sarkin Fulani shugaban APC na jiha dake tafe ya ce “shugabanin jam’iya da sakatororinsu a matakin ƙananan hukumomi muna godewa Allah da ya haɗa mu a wannan wurin domin tattauna abubuwan da suka shafi tafiyar jam’iyarmu da cigaban Sakkwato da farko ina godiya gare ku kan goyon bayanku gare mu don cigaban APC.

“A matsayina na Sanata dake waƙiltarku ba zan taɓa yarda na ci amanarku ba, duk abin da zan gaya maku gaskiya ce ba yaudara, ko ba komai nasan zan haɗu da Allah, gudunmuwar da nake ba ku sai abin da ya ci gaba,” a cewarsa.

Ya ƙara da cewa “ina son na yi magana da matasa halin da muke ciki ba damar mu cigaba da faɗa da tashin hankali kan siyasa musamman a yankin da muka fito ‘yan uwanmu suna kwana da tsoro da firgici ba su kwana da kwanciyar hankali wannan za mu mayar da hankali ko faɗan siyasa yakamata mu canja siyasar da ake yi baya, in muka yi haka za mu samu shugabanni nagari, akasin haka za a cigaba da yaudarar ku, duk wanda ya yi ciniki da kai ka shiga tafiyarsa ka san akwai buƙatar da yake da ita,  mai yin siyasar cin zarafi ba don cigaban matasa yake yinta ba.

“Ina jawo hankalin ku matasa duk abin da za mu yi mu auna shi da addininmu ba da son rai ba, wannan damuwar da muke da ita na rashin samun shugabanni ne nagari, laifin masu zaɓe ne, duk wanda zai ce sai nagari shi ne yafi domin shugabanni nagari ne kaɗai za su iya samar da tsaro da Asibiti mai inganci da ilmi mai kyau da zaran waɗan nan suka samu ba abin da mutum zai yi da kuɗi.

“Duk kuka cigaba da yin wannan abin na neman dukiya a harkar zaɓe ba za a samu kuɗin ba kuma cigaban ba zai samu ba, don haka ina baku shawara matasa ku zo mu haɗa kai mu yi siyasa ta gaskiya da amana, banda sha’awar naga mutum ya ɗauki ko tsinken tsintsiya da nufin dukar wani ban tare da duk mai yi Allah ne sheda ,” kalaman Lamiɗo.

Hakan ke nuna jam’iyar APC a Sakkwato bangarori biyu ne suka gudanar da zaɓen shugabanni, ɓangaren gwamnatin jiha wadda Sanata Aliyu Magatakarda ke jagoranta da kuma gefen da Sanata Ibrahim Lamiɗo ke jagoranta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here