Gwamnan Kebbi ya ba da kyautar miliyan 30 ga hukumar Zakka ta jihar
Gwamnan Jihar Kebbi Dakta Nasir Idris (Kauran Gwandu) ya kai Sadakar kudi naira Million 30 ga hukumar Zakka da Waqafi ta Jihar Kebbi Ƙarkashin Jagoranchin Mallam Umar Isah Birnin Kebbi In da ya karɓi Wannan Saƙon ga kwamitin da aka kafa domin hannunta Ƙuɗaɗen wanda Alhaji Usaman Abubakar Tarasa ya jagoranta.
Sadakar ana zaton za a rabawa marasa karfi a jihar domin samun saukin ibadar azumi a watan Ramadan






