A ƙalla mutane uku ne aka kashe aka yi garkuwa da mace ɗaya a wani harin dare da ‘yan bindiga suka kawo a garin Bargaja ƙaramar hukumar Isa jihar Sakkwato.
Majiyar da ta yi magana da waƙilinmu ta ce an kawo harin ne 1:20 na daren ranar Litinin, maharan sun shammaci mutanen garin suka shiga ciki in da suka fi ƙarfin ‘yan sakan garin.
“Koda can muna karɓar rahoto daga ƙauyukka maƙwabtanmu kan abin da ya shafi zuwan ‘yan bindigar amma a wannan karon ba mu samu bayanin ba, mutane uku da suka kashe maza ne kafin su yi nasarar tafiya da mace guda,” a cewarsa.
Majiyar ta ce mutanen suna cin karensu ne ba babbaka saboda babu isassun jami’an tsaro a yankin, ya kira hukumomin da abin ya shafa su tashi tsaye don kare rayuwa da dukiyoyin jama’a.
Mutanen yankin suna zargin ko an kira jami’an tsaro dake kusa ga ƙauyen ba su zuwa domin ba da ɗauki halin da yakamata a sauya shi.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Sakkwato DSP Rufa’i Ahmad ba a samu magana da shi ba kan harin domin wayarsa ba ta zuwa.





