Home Rahoto ’Yan Bindiga Sun Nemi Naira Miliyan 100 Daga Wajen Al’ummar Kebbi

’Yan Bindiga Sun Nemi Naira Miliyan 100 Daga Wajen Al’ummar Kebbi

2
0

Rahotanni daga yankin Kebbi ta Kudu sun nuna cewa ’yan bindiga da ke addabar wasu sassan yankin sun nemi kuɗin haraji har Naira miliyan 100 daga al’ummar ƙauyen Utouno da ke Ƙaramar Hukumar Ngaski.

A cewar majiyoyin cikin gida ’yan bindigar sun yi barazanar kai hari ga al’ummar ƙauyen idan ba a biya kuɗin ba, lamarin ya jefa mazauna yankin cikin fargaba da tashin hankali.

Wannan barazana na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren garkuwa da mutane, satar shanu, da kai farmaki kan ƙauyuka
ke ci gaba da ƙaruwa a wasu sassan Arewa maso Yamma.

Har yanzu ba a fitar da cikakkiyar sanarwar hukuma daga hukumomin tsaro ba kan lamarin, amma ana sa ran za a ƙara tsaurara tsaro a yankin domin kare rayuka da dukiyoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here