Alhaji Buhari Sidi Attahiru Sokoto jigo a jam’iyar ADC a sakkwato da Nijeriya ya yi magana kan halin da jam’iyar take ciki da bincikar Tambuwal a badaƙalar kudi biliyan 117 da sauransu a hirarsa da waƙilinmu.
Ya kake kallon tasirin jam’iyar adawa ta ADC da jagoranta Sanata Aminu Waziri Tambuwal a Sakkwato
Jami’iyar adawa ta ADC a Sakkwato ka ga irin tsare-tsaren da ake ciki a yanzu na tabbatar da ta tsayu da ƙafafunta ne, tasirinta zai bayyana da har za a yi magana kansa anan gaba kaɗan. Tasirin Sanata Tambuwal ne ya kawo karsashi da tsimayen tafiyar a jiha, alƙalumma da muke da su mu ‘yan siyasa in ka duba muna da gwamnoni biyu da suka gabata kafin Tambuwal waton Alhaji Attahiru Bagaruwa da Sanata Aliyu Wamakko, a yau jagororin siyaasa biyu ne a jiha ko kana gidan Tambuwal ko Wamakko domin shi Bafarawa ya ce yabar siyasar jam’iya uba ne, tafiyar Tambuwal tafi karɓuwa ga mutanen Sakkwato musamman masu ilmi da suka san ciyon kansu da hangen nesa, su ne ke kallon Aminu matsayin jagora za ka samu masu mutunci sun fi yawa a tafiyarsa, za ka tabbatar da haka daga yanda yake fitar da masu takara yana da bambanci da Wamakko, shi ne ya sa talaka ke son tsarinsa don yana yin abin da yake so, dubi waɗanda ke riƙe da mukƙamai a gefensa, yanda ake cin amfaninsu a jiha fiye da waɗanda ba su ba. A dimukaraɗiya mutanen Tambuwal ne kake ji ana amfana da su ana yi masu addu’a da fatan alheri, ba wanda ake kira masu zango ɗaya za ku yi, saboda suna da tsari da ilmi da kyakkyawar mu’amala wannan na cikin abin da ya janyo wa Tambuwal tasiri fiye da duk wani jigo da ake da a jihar Sakkwato.
Kwamitin da gwamnatin Sakkwato ta kafa kan bincikar gwamnatin Tambuwal ta gano an yi sama da faɗi da biliyan 117 ya kake kallon rahoton da kwamitin
Allah na gode ma, da a Sakkwato na tashi, wannan tsarin da suka yi an yi a baya lokacin gwamnatin Wamakko aka kai Bafarawa kotu aka tsare shi na lokaci, abin da aka yi ba mu ga fa’idarsa ba, don ba a ga abin da aka karɓa ga Bafarawa ko ya maida ba, tsakaninsu waye ya yi nasara, babu wani cikakken bayani kan matsayar da aka cimma, maganar ta ƙare yana tare da iyalansa cikin ƙoshin lafiya, abin ya zama tarihi ba a maidawa jiha komai ba irin abin da ake wa Tambuwal ɗaya ne domin jagora ɗaya ne ke son a yi haka bita da ƙulli ne kan yaƙi da ‘yan adawa yakamata su sani duk wani mai yin dimukaraɗiya dole ya haɗu da adawa, muna ƙalubalantarsu da su baiwa Tambuwal damar kare kansa, a daina yi masa jawo rufe, domin mu talakawa mun san Tambuwal ya kashe mana kuɗinmu kan ƙa’ida, ko kotu aka tafi za mu ba da shedar mu(Sakkwatawa) aka kashewa kuɗin. Cin zarafin da ake son yi masa ba zai yiwu ba da ikon Allah mu ne za mu kafa gwamnati.
Ana zargin APC za su karya jagororin adawa a jihohinsu in hakan ya faru a Sakkwato in kama Aminu Tambuwal za ku ji tsoro ku mabiyansa.
Ai na gaya maka kafin Tambuwal ya jagoranci Sakkwato an samu matsalar taɓarɓarewar tarbiya da rashin jagoranci mai kyau in da har mutane sun yi ta roƙon Allah samun sauyi, bayan ya zo ya fuskanci matsalolin da ke fuskantar mu musamman bangar siyasa, in da ya ci ƙarfin su sosai, akwai abubuwa da yawa da ya yi daidai da buƙatun mutane jiha kama da biyan kuɗin makarantar yara da bayar da tallafi daban-daban da inganata lafiya da ilmi hakan ya sa ya shiga cikin zukatan mutanen jiha, ko an yi masa abin da ake zargi in shi ke takara ko ya tsayar da wani a hasashen da ake da shi zai ci zaɓe ko baya nan domin nagartattun mutane yake hulɗa da su, akwai fahimta tsakanin Tambuwal da mutanen Sakkwato, ba zai goyi bayan wanda ba mutane ba ne gabansa ba.
Shekara uku na gwamnatin Sakkwato amma har yanzu akwai matsalar ruwan sha birnin jiha wace shawara za ka baiwa gwamnati.
In za su yi amfani da shawara ta su koma baya su bincike gwamnatin Aminu Waziri kan hanyoyin da suka bi wajen wadatar da ruwa a birnin Sakkwato ko su tutuɓi tsohon Kwamishinan ruwa, bayar da ruwan sha na cikin abubuwan da suka yi yekuwar zaɓe kanta, kafin a basu gwamnati an yi maganin matsalar da kashi 70 amma yanzu abin ya taɓarɓare fiye da baya, in suka ce ba za su yi aiki kan aikin Tambuwal, ba za su yi nasara ba har a ƙwace gwamnatin, kar su manta aikin al’umma dole ka ɗaura saman na wani, don a yi nasara, fatar mu mutanen Sakkwato su samu ruwa.
Ana yawo da magana a Sakkwato cewa ku ‘yan adawa kuna tsoron gwamnati mai ci don haka kuka laɓe ba motsi
Mi zai sa mu ji tsoron ta, a yanzu tana cikin shekara ta uku, in kana son ka yi adawa ta tsakani da Allah ya kamata ka baiwa Gwamnatin da aka zaɓa dama ta yi abin da ta yi alƙawarin za ta yi wa mutane, saura watanni a dawo neman mulki sai mu ɗaura gwamnatin a sikeli kowa ya ga abin da ta yi, aiyukkan Tambuwal na shekara biyu wannan gwamnati ba za ta iya yinsu a shekara huɗu ba, duk abin da suka soki Gwamnatin Tambuwal kansa ga shi sun kasa komai kan shi kama daga matsalar tsaro da ruwan sha da sauransu. Ga matsalar sanya mutane kan madafun iko ba tare da cancanta ba, ga kuma mayarda sarakuna da ma’aikatan gwamnati mambobin jam’iyar APC a jiha, matukar aka ci gaba da haka cibaya za a samu, a wannan karon lalle mu ne masu nasara da ikon Allah za mu ci zabe domin wanda ya yi maka alkawali bai cika ba, kana da damar canja shi.
Ka sani duk abin da yake na alheri ne sai ya zo da jarabawa, kar ka manta a cikin jam’iyar ADC fa wasu aka sama ka ga dole wasu za su rasa kujerunsu wasu za su sauya mukamai ka ga ‘yan adam ne mu, in dai har su Tambuwal ne za su jagoranci tafiya rigimar mukami a ADC ba komai ba ne za a gyara shi a tafi tare da kowa don samar da mafita ga jihar Sakkwato da Nijeriyag.



