Home Manyan Labaru Yakamata shugabannin Arewa su kira taro kan matsalar tsaro da batun sojojin...

Yakamata shugabannin Arewa su kira taro kan matsalar tsaro da batun sojojin Amerika da ƙabilanci—-Farfesa Mansur Ibrahim

4
0

Yakamata shugabannin Arewa su kira taro kan matsalar tsaro da batun sojojin Amerika da ƙabilanci—-Farfesa Mansur Ibrahim

Shugaban riƙo na majalisar Muslim Solidarity a Sakkwato Farfesa Mansur Ibrahim Sa’id ya bayyana buqatar da ake da ita ga shugabannin Arewa a wannan lokacin da abubuwa ke qara lalacewa a yankin.

Farfasa Mansur a satin da yagabata wurin taron majalisar na shekara wanda aka gudanar a xakin taro na jami’ar Xanfodiyo a Sakkwato ya fitar da qalubalen da Arewa ke fuskanta wanda ba zai yiwu a yi shiru ko zuba ido ba, gudun kar a faxa halin mai muni fiye da wanda ake ciki.

“Yakamata shugabanin Arewa su kira taro kan matsalar tsaro da zawan sojojin Amerika da faxan qabilanci waxannan abubuwan suna qara kassara Arewa dole shugabanni su haxa kai su yi matsaya guda da murya xaya a warware damuwar.”

Farfesa ya ce gwamnatin Nijeriya da ta jihohi su samr da tallafi ga manoman domin halin da ake ciki harkar noma na mutuwa a Arewa saboda karyewar farashin abinci, kayan noma na tsada amma abinci yana rahusa, ba wani manomi da yake yin noma a Arewa a yanzu dake cin riba a harkar, bai kamata a bari hakan na samun koma baya ba, ina kira da gwamnati ta samar da tsarin tallafawa manoma ta hanyar ba su abin noma kyauta a kuma sayi kayan da suka noma da farashi mai tsoka savanin na kasuwa.

Farfesa Sa’aid da ya juya kan kalaman uwargidan shugaban qasa kan hare-haren da Amerika ta kawo Arewa ya ce “mun yi alawadai ga maganarta domin ba ta nuna tana tare da mu ba, muna kira ta janye kalaman da ta yi.”

Ya ce bai kamata uwa ta goyi bayan kashe ‘ya’yanta ba, mu mutanen Arewa ‘ya’yanta ne don haka ta riqa mu ba wani bambancin addini.

Taron ya samu halartar dukkan manyan malaman jihar Sakkwato kuma sun tofa albarkacin bakinsu tare da qarfafa kalaman shugaban majalisar da goyon bayansa.    

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here