Wani jigo a jam’iyyar ADC a Jihar Rivers, Sunday Ohakwu, ya yi zargin cewa akwai wani shiri na kama Rotimi Amaechi, tsohon minista kuma mai neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
Ohakwu ya ce jam’iyyar APC na fargabar ƙaruwa da farin jinin Amaechi, kuma ana ƙoƙarin amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci kamar EFCC da ICPC da DSS domin cafke shi.
Ya ce an gudanar da tarurruka domin samo hujjojin da za su kai ga kamawa da gurfanar da Amaechi, amma ya jaddada cewa duk wani yunƙurin tsoratar da su ba zai yi nasara ba.
Amaechi, tsohon gwamnan Jihar Rivers, na neman shugabancin ƙasa a ƙarƙashin ADC.






