Jaruma Hadizan Saima Ta Cika Shekaru 34 A Duniya
Jaruma a masana’antar Kannywood, Hadiza Muhammad wacce aka fi sani da Hadizan Saima, ta cika shekara 34 a Duniya, kamar yadda ta bayyana wa gidan rediyon Kano, Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.
Hadiza Muhammad ta ce tana da shekara 13 a lokacin da ta fara fim. A yanzu haka ta kwashe shekara 20 tana harkar shirya fina-finan Hausa, wanda hakan ke nuna cewa a wancan lokacin tana da shekaru 33 cif-cif a Duniya.
Wannan na nufin ita sa’a takwarorinta jarumai ne irin su Hadiza Gabon, Fati Washa, Rahma Sadau da Nafisat Abdullahi.
Ta bayyana hakan ne a shekarar da ta gabata, kuma yanzu haka tana da shekaru 34 a Duniya.
i





