Kisan uwa da ‘yayanta a Kano: ‘Yansanda sun kama dan ‘yar uwar marigayiyar da wasu mutane 2 da ake zargi da kisan
Rundunar ’Yansanda ta jihar Kano ta kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisan gillar wata uwa da ’ya’yanta shida da aka yi a unguwar Dorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Lahadi.
Kamen ya biyo bayan wani aiki na musamman bisa bayanan sirri, wanda aka gudanar bisa umarnin sufeto janar na ’Yansanda, Kayode Egbetokun, tare da kulawar kwamishinan ’Yansanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori.
A cewar rundunar, an kama wadanda ake zargin ne a wani samame da aka gudanar daga karfe 10:00 na dare a ranar 17 ga Janairu zuwa karfe 4:00 na asubahin ranar 18 ga Janairu, 2026.
Wadanda aka kama sun hada da Umar Auwalu, mai shekaru 23 daga unguwar Sabuwar Gandu; Isyaku Yakubu da aka fi sani da “Chebe”, mai shekaru 40 daga unguwar Sagagi; da Yakubu Abdulaziz wanda aka fi kira “Wawo”, mai shekaru 21 daga unguwar Sabon Gida Sharada.
’Yansanda sun bayyana cewa wanda ake zargin jagorantar kisan, Umar Auwalu, wanda dan uwa ne ga marigayiyar, ya amsa laifin aikata kisan. Haka kuma, ya bayyana cewa sun aikata wasu kashe- kashe masu tada hankali a wasu sassan Kano a baya-bayan nan.
Daga cikin abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin akwai tufafi masu tabon jini, wayoyin salula biyu na marigayiyar, adda, gora, kudi da ake zargin an kwace a wajen da abin ya faru, da wasu makamai masu hadari. Rundunar ta ce bincike na ci gaba.
Rundunar ’Yansanda ta Jihar Kano ta yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da gode wa al’umma bisa addu’o’i, goyon baya da hadin kai. Rundunar ta kuma tabbatar wa jama’a kudirinta na ganin an gurfanar da duk masu aikata laifuka a gaban kuliya.






