Home Siyasa Majalisar dokokin Rivers ta gaza sake zama don tattauna batun tsige gwamnan...

Majalisar dokokin Rivers ta gaza sake zama don tattauna batun tsige gwamnan jihar

7
0

Majalisar dokokin jihar Rivers a ranar Talata ta gaza sake zama domin zaman majalisa da ake sa ran yi kan batun tsige gwamna Siminalayi Fubara, lamarin da ya kara jefa alamar tambaya kan shirin tsige gwamnan.

’Yan majalisar ba su bayyana a harabar majalisar ba, inda dakin majalisar ya kasance a kulle.

Wannan ya kara tayar da hankula a jihar, wadda ke fuskantar rikicin siyasa sakamakon takaddama tsakanin Gwamna Fubara da magabacinsa, Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja.

Ko da yake babu wata sanarwa a hukumance daga shugabancin majalisar, majiyoyi sun ce jinkirin na da nasaba da sabanin cikin gida tsakanin ’yan majalisar da kuma matsin lamba na siyasa.

A makon da ya gabata ne rahotanni suka bayyana cewa majalisar na shirin fara tsige gwamnan bisa zargin aikata manyan laifuka, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce da gargadi daga masana shari’a da kungiyoyin farar hula kan bin ka’idojin doka.

A halin yanzu, tsaro ya tsananta a kusa da harabar majalisar, yayin da al’ummar jihar ke kira da a yi tattaunawa da nuna hakuri domin kauce wa kara dagula rikicin siyasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here