An hangi Akor Adams yana girmama marigayi Patrice Lumumba, Firayim Ministan farko na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo), bayan ya zura ƙwallo a wasan daf da karshe (kwata fainal) na gasar Kofin Nahiyar Afirka ta 2025 (AFCON).
A ranar Asabar, Adams ya ci ƙwallo ta biyu a nasarar da Najeriya ta samu da ci 2–0 a kan Algeria.
Wannan ƙwallon ita ce ta biyu da ɗan wasan mai shekaru 25 ya ci a gasar, sannan ita ce ta huɗu da ya ci wa tawagar Super Eagles gaba ɗaya.
Bayan zura ƙwallon, Adams ya tsaya ya ɗauki wani salo da ya yi kama da gumakan Patrice Lumumba da ke babban birnin DR Congo, Kinshasa.
Wannan salon Lumumba ya shahara ne ta hannun Michel Nkuka Mboladinga, wani masoyin ƙwallon ƙafa daga DR Congo da ya halarci dukkan wasannin ƙasarsa a AFCON 2025. Ya rika sanya kaya kamar na shugaban farko na ƙasarsa, yana tsayawa cak a kan wani dandali a kowane wasa.
Michel Nkuka Mboladinga yana ɗaukar salon gumakan Patrice Lumumba.
Lumumba shi ne Firayim Ministan farko na DR Congo, kuma an kashe shi a shekarar 1961. Tun daga lokacin, ya kasance ɗaya daga cikin fitattun jaruman siyasa da Afirka ke girmamawa.



