Home Uncategorized Mata Sun fi maza kokari a Makarantun katsina—Kwamishina Ilimi na Jihar Katsina

Mata Sun fi maza kokari a Makarantun katsina—Kwamishina Ilimi na Jihar Katsina

121
1
 
Daga Rafi’atu Mustapha Katsina.
 
Kwamishinan Ilimi na Jihar Katsina, Farfesa Badamasi Lawal, ya ce dalibai mata sun yi zarra kan takwarorinsu maza a jarrabawar kammala sakandare da aka rubuta a jihar a bara.
 
Farfesa Lawal ya bayyana haka ne a wajen bikin rufe shirin bai wa ’ya’ya mata ilimi (GEP-III) da aka gudanar a jihar ranar Alhamis.
 
Ya ce an cim ma wannan nasarar ne sakamakon muhimmancin da gwamnatin jihar ta bai wa ilimin ’ya’ya mata ta hanyar samar da shirye-shiryen ilimantar da su.
 
A cewar jami’in, dalibai 18,321 ne suka rubuta jarrabawar WASSCE a fadin jihar a bara wanda gwamnatin jihar ta dauki nauyin biya, Ya kara da cewa, “Daga cikin adadin daliban da suka rubuta jarrabawar, maza 10,441 ne, sannan mata 7,880. 
 
“Sakamakon jarrabawar ya nuna 4,627 daga cikin dalibai mata sun samu makin ‘credit’ a darasin harshen Turanci, wato kwatankwacin kashi 58.7 cikin 100 ke nan.
 
“Yayin da a cikin dalibai maza su 10,441, mutum 5,632 ne suka samu makin ‘credit’ a darasin harshen Turanci, wanda ya yi daidai da kashi 54 cikin 100.
 
“Hakan ke nuna matan sun fi mazan kokari a darasin harshen Turanci.
 
“A bangaren darasin Lissafi ma matan sun fi mazan kokari, domin kuwa mata 5,678 ne suka samu makin ‘credit’, inda ake da maza 4,726 da suka samu kwatankwacin makin,” in ji kwamishinan.

1 COMMENT

  1. Hi,

    We recently tried reaching out via https://www.instagram.com/tagdiv but aren’t sure our message got through.

    After reviewing Managarciya Com, we thought your brand could be a strong fit for Grace Belgravia and wanted to personally extend an early access invitation.

    Founded in London, Grace Belgravia is a new influencer and creator management platform designed to help brands discover creators, organise campaigns, protect content rights and measure results from one place.

    Brands can invite influencers both on and off platform, manage collaborations, automate agreements, oversee content delivery and track campaign performance through a single dashboard.

    As part of our early beta launch, you can use code EARLYACCESS to get the Self Service plan completely free for your first 2 months. The voucher is valid for the next 30 days.

    Create your free early access account here:

    https://gracebelgravia.com

    If creator partnerships, influencer marketing or social media collaborations are handled by another member of your team, we’d be grateful if you could forward this invitation to them.

    Best regards,

    Grace Belgravia

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here