A lokacin da zaben 2023 ke matsowa wadanda ke son tsayawa takara suna cigaba da neman goyon baya a tsakanin magoya bayan jam’iyyunsu daban daban.
PDP a jihar Jigawa sun goyin bayan takarar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wanda ake saran zai fito takarar a wannan zaben mai zuwa.
Shugaban jam’iyar a jihar Jigawa Honarabul Babandi Ibrahim Gumel ya sanar da matsayar jam’iyar PDP a jihar cewa Atiku ne za su marawa baya a zaben 2023.
Babandi ya ce Atiku ba ya da wata matsala a jihar Jigawa shi ne zabinsu domin ba ya da wata matsala da jagoran jam’iyar PDP a jihar Jigawa waton tsohon gwamnan jihar Sule Lamido.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da kungiyar neman goyon baya ta Atiku Abubakar ta ziyarci jihar in da aka gabatar da taro a hidikwatar jam’iya.





