Home Siyasa
12
0

Dalilina na barin APC na koma ADC—-Tsohon Ciyaman Na Tangaza

Honarabul Isah Salihu Kalanjeni ya bayyana dalilinsa na barin APC ya koma ADC saboda ba wani cigaba da ya samu daga sanda ya koma jam’iyar.

Ya ce yana nan in da yake tun sanda ya shiga jam’iyar in da ya tuma nan ya fada.

  Ya kara da cewa duk wanda ya sani ya san hulda ta da Tambuwal tsawon shekarru 16 zuwa 20, abin da ya faru tsakaninmu sharrin shedan ne, domin in da na tuma nan na fadi ciyaman na bari a PDP shi ne aka bani a APC shima dakyar kafin na samu.

“Ina mai baka hakuri game da wannan tafiya ta ADC akwai jarabawowi, amma Allah ya saka maka duk in da nasara take sai an samu jarabawa.”

“Na shigo wannan tafiya ba gudu ba ja da baya, don nasan ba wanda ke bayarwa sai Allah,” a cewar Kalanjeni.

Da ya juya kan matsalar tsaro ya roki Allah ya kawo sauki ya yi mana ganinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here