2027: Ubandoma da Faruku Yabo Sun Gana a Abuja

2027: Ubandoma da Faruku Yabo Sun Gana a Abuja

Alhaji Sa'idu Umar Malam Ubandoma wanda ya yi wa jam'iyar PDP takarar Gwamna  a zaben da ya gudana na 2023 ya gana da Ambasada Faruku Malami Yabo a gidansa dake Abuja.
'Yan siyasar biyu sun hadu ne kwana daya kafin babban taron shugabanin jam'iyar PDP da za a gudanar a ranar Laraba.
Masu sharhi a jiha sun danganta haduwar nada nasaba da yanda shugabannin rikon kwaryar da jam'iyar za ta Sanya za su tafiyar da jam'iyar domin samun nasarar tafiyar jam'iya a kakar Zabe na gaba.
Malam Ubandoma da Faruku Yabo abokan juna ne da ake ganin kowanensu na iya mara baya ga  takarar Gwamna ga daya, in ya samu nasarar samun tikitin takara a jam'iyar PDP a 2027.