2027: Tinubu Zai Iya Ganin Adawar da Bai Taba Gani ba a Siyasa, Ana Shirin Kifar da Shi 

2027: Tinubu Zai Iya Ganin Adawar da Bai Taba Gani ba a Siyasa, Ana Shirin Kifar da Shi 


Wasu kungiyoyi da jam'iyyun adawa sun fara shirin zakulo hanyoyin tumbuke Bola Tinubu a 2027. Ana hasashen jam'iyyun da kungiyoyi za su yi wata irin haɗaka da ba a taba yi ba domin kifar da Bola Tinubu a zaben 2027. 
Vanguard ta ce dan Majalisar Tarayya, Hon. Ikenga Imo Ugochinyere ya ce sun shirya haɗaka mai ƙarfi domin tunkarar 2027. 
Hon. Ikenga ya ce jam'iyyun adawa za su yi gagarumar haɗaka ko da jam'iyyar PDP ko babu ita domin samun nasara a zaben. Ugochinyere ya ce PDP ta gaza samar da adawa mai karfi a daidai lokacin da kasar ke fuskantar barazana. 
Dan Majalisar ya soki gwamnonin PDP kan nuna goyon bayansu ga shugaban jam'iyyar, Umar Damagum. Ya zarge su da yi wa Ministan Abuja, Nyesom Wike aiki domin ganin PDP ba ta sake tasiri ba a matsayin jam'iyya mai karfi.