Daya daga cikin Jigogin jam'iyar PDP a jihar Sakkwato Honarabul Buhari Sidi Attahiru ya yi magana kan Sanata Ibrahim Lamido da yadda yake ganin cancantarsa ga zama gwamnan Sakkwato.
Honarabul Buhari yana da yakinin wannan tafiyar ta Sanata Lamido za ta haifar da cigaba a jihar Sakkwato kamar yadda ya soma a wakilcin da yake yi wa Gabascin Sakkwato.
"Hanyar Sanata tana bullewa kasan akwai bambanci tsakanin mai nema wurin wani da mai nema ga Allah, shi Lamido na kokarin yin abin da ya yiwa al'umma alkawali, saboda hakan Allah zai ba shi nasara, ai an taba samun irin haka a baya a nan Sakkwato lokacin da Sanata Wamakko ya zama gwamna bai tare da Gwamna a lokacin, kuma dukan jagorori a lokacin ko daya basa goyon bayansa, amma Allah ya ba shi mulki.
"Karfin da Lamido ya shigo da shi a siyasa a lokacin da Wamakko ya shigo bai da irin wannan karfin, kuma Allah bai hana shi ba, abin da ke gaban mutum ya yi abin da ya dace sauran lamari ka barwa Allah, bana ganin sun isa su hana shi cin nasara abin da zai yi don suna da mulki, ana iya kayar da gwamna a lokacin da yake saman kujera, yanzu ba lokacin kamfe ba ne amma ba kujerar gwamna ba ko ta Shugaban kasa Lamido ya nema muna yi masa fatar alheri da rokon Allah ya tabbatar da shi kanta don ya cigaba da yin aiyukkan alheri da yake yiwa jama'a." a cewar Honarabul Buhari.