Home Labarai 2027: Majalisar  Shari’ar Musulunci ta buƙaci a gaggauta cire Shugaban Hukumar Zaɓe 

2027: Majalisar  Shari’ar Musulunci ta buƙaci a gaggauta cire Shugaban Hukumar Zaɓe 

11
0

Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci ta buƙaci a gaggauta cire Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, daga mukaminsa, tana mai cewa ba za ta amince da duk wani zaɓe da aka gudanar ƙarƙashin jagorancinsa ba.

Shugaban majalisar, Farfesa Sheikh Bashir Aliyu, ya bayyana cewa mutumin da ake zargin mutuncinsa da amincinsa yana cikin shakku ba zai iya gudanar da zaɓe mai inganci da adalci ba.

Majalisar ta ce cire shugaban INEC ya zama wajibi bisa zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma damuwar da ake nunawa kan sahihancin rajistar masu zaɓe, musamman ikirarin cewa ana iya yin maguɗi wajen sauya adadin masu rajista.

Sheikh Bashir ya jaddada cewa Najeriya na buƙatar shugaban hukumar zaɓe wanda mutuncinsa, tsaka-tsakinsa da gaskiyarsa ba su da wata shakka.

Majalisar ta kuma yi gargaɗin cewa rashin amincewa da shugabancin INEC daga wasu ɓangarorin ƙasa na iya raunana amincewar jama’a ga zaɓukan da za a gudanar, musamman zaɓen shekarar 2027.

–MIKIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here