“Kaso 85 Na Ƴan Arewa Sun Karkata Ne Ga Zaɓar Atiku Abubakar A Matsayin Shugaban Ƙasa A Zaɓen 2027”. In Ji Binciken Masana
Wani bincike da masana siyasa da rayuwar al’umma suka fitar ya nuna cewa ƴan Najeriya musamman ƴan Arewa ba su da ƙarfin gwiwar sake zaɓar Tinubu 2027 saboda matsalolin rashin tsaro, tsadar rayuwa da rashin sauraron jama’a da gwamnatin Tinubu ke yi.
A cewar rahoton, duk da yadda gwamnatin Tinubu ke kashe maƙudan kuɗaɗe wajen jan ra’ayin wasu malaman addini da masu tasiri a Media domin su tallata gwamnatin hakan bai yi wani tasiri na a zo a gani ba.
Rahoton ya ƙara da cewa kaso 80 na matasa a Arewa ba su da aikin yi. Sannan sama da kaso 90 na gidaje ba sa iya cin abinci sau uku a rana saboda rashin kuɗi da tsadar rayuwa da taɓarɓarewar harkokin noma. Sannan matsalar tsaro ta shafi gidaje da dama, wasu sun rasa iyayensu, wasu ƴan’uwansu wasu ƴaƴansu; an kashe su ko an yi garkuwa da su.
”Dawo da tallafin mai, sauƙaƙa rayuwar talakawa su riƙa samun abinci sau uku, da samar da tsaro. Su ne matakan da gwamnatin Tinubu za ta ɗauka ta kai ga nasara. Amma in ba wannan matakan ba akwai iyuwar ƴan Najeriya musamman ƴan Arewa su zaɓi Atiku a zaɓen 2027 musamman ma saboda alƙawarin dawo da tallafin mai da ya yi”. In ji rahoton.
Shin kana ɗaya daga cikin ƴan Arewa da zasu zabi Atiku Abubakar ɗin ?






