An samu tsaiko a harkokin gudanarwa a Jihar Kano bayan Gwamna Abba Yusuf ya umarci ma’aikatun gwamnati da hukumomi (MDAs) da su daina aika fayal zuwa ofishinsa har sai an ba da wani umarni na gaba.
An bayar da wannan umarni ne a daidai lokacin da gwamnan ke mayar da hankali kan tarurrukan siyasa a Kano da Abuja, domin shirye-shiryen sauya sheƙarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Farouk Ibrahim, ne ya sanar da kwamishinoni wannan umarni a ƙarshen taron majalisar zartarwa ta Jihar da aka gudanar a ranar 18 ga Disamba, 2025, wanda gwamnan ya jagoranta.
DAILY NIGERIAN ta gano cewa tarin fayal da ba a duba ba da suka taru a dadar Gwamnatin Kano tun daga watan Satumba an mayar da su zuwa ma’aikatun gwamnati, sassa da hukumomi.
Wata majiya daga ciki, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa wannan jarida cewa wannan mataki ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihin Jihar Kano.
“Ina aiki a Fadar Gwamnati ƙarƙashin gwamnoni da dama, amma ban taɓa ganin lokacin da aka hana karɓar fayal ba.
“Tsawon makonni, ba a karɓi ko fayil ɗaya a rijistar fadar gwamnati ba. Wannan shi ne karo na uku da gwamnan ya ba da umarnin hana ma’aikatun gwamnati da hukumomi aika fayiloli. Wannan tsari ne na rufe harkokin gwamnati.
“Wataƙila wasu daga cikin fayal da ke jiran gwamnan sun shafi buƙatar sayen magunguna ko kuma gaggawar lafiya” in ji majiyar.
Wani babban lauya a Kano, Sagir Gezawa, ya bayyana matakin gwamnan a matsayin watsi da nauyin da ya rataya a kansa, yana mai cewa ƙin karɓar fayal na da illa ga walwalar zamantakewa da tattalin arziƙin jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farouk Ibrahim, bai samu damar yin tsokaci ba domin lambar wayarsa da aka sani a kashe take a lokacin da ake kammala wannan rahoto.






