2027: Atiku da Obi Sun Gana a Abuja
Pita Obi ya kai ziyara zuwa ga Atiku Abubakar a gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja Najeriya.
Atiku Abubakar da Pita Obi Dukkan sun tsofafin yan takara shugabancin Najeriya ne a jam'iyu PDP da LP a zaben da ya gabata na 2023 inda dukan su suka sha kasa a hannun Shugaban kasa Ahmad Bola Tinubu na Jam'iyar APC.
Wannan ziyara dai akan fassara ta da abubuwa daban daban da suka shafi Siyasa, Hadin kai da kuma ƙawance duk da dai su basu fadi makasudi haduwar ba.
Masu fashin bakin siyasa sun ce a 2023 da an hada kuri'u Obi da Atiku da sun rinjayi kurii'un Bola Tinubu.
Shin ko Atiku da Obi zasu iya hada kai ne domin tun karar Bola Tinubu a zaben 2027 ko kuma kowa zaiyi takansa.
managarciya