2027: Abin da haduwar Sanata Lamido da Faruku Yabo  a Abuja ke nufi

2027: Abin da haduwar Sanata Lamido da Faruku Yabo  a Abuja ke nufi


Sanata Ibrahim Lamido da Ambasada Faruku Malami Yabo Sun hadu a Abuja yayin gudanar da sallar Jumu'a.
Haduwar ta 'yan siyasar ita ce irinta ta farko a bainar jama'a in da ake kallonta da akwai abin da ke shirin faruwa a siyasar Sakkwato.
Sanata Lamido Dan siyasa ne da yake kokarin faranta rayuwar al'ummar jiha ba tare da la'akari da yankin da yake wakilta a majalisar dattijai, wannan halin ya sa mutane sun fara yi masa fatar zama Gwamnan Sakkwato a kakar Zabe Mai zuwa.
Ambasada Faruku Malami Yabo yana da karbuwa a siyasar Sakkwato ganin yanda yake Mai kyauta da wayewa da yake da ita a harkokin zamani da kasuwanci.
Masu sharhi sun fara hasashen wata dangataka ce ta siyasa aka kulla a tsakanin 'yan siyasar wadda za ta haifar da Wani sauyi a siyar Sakkwato nan gaba kadan.
Siyasar Sokoto za ta zo da abubuwan da ba a Saba gani ba, in da soyayyarka da jama'a da taimakonsu ne kawai zai taimakeka ga samun  kuri'unsu.