Tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki Da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad ne kwamitin dattawan Arewa suka zaba su yi takarar shugaban kasa daga Arewa.
Wannan matsayar an cimma ta ne a yunkurin da Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da Muhammad Hayatudeen suka cimma na aminta da hada hannu tun a baya tare da wadanda aka zaba domin samar da dan takara guda da zai wakilci yankin Arewa.
Farfesa Ango Abdullahi ne ya jagoranci kwamitin tantancewar kashi uku.
Sanarwar ta kara da cewa “A bisa manufar wannan tantancewar, an yanke shawarar cewa Gwamna Bala Mohammad daga yankin Arewa maso Gabas da kuma tsohon shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki daga yankin Arewa ta tsakiya, za a gabatar da su a matsayin ‘yan takarar maslaha na Arewa a yanzu.
“An yanke shawarar cewa a gabatar da wani jigo daga Arewa ta Tsakiya da kuma daya daga Arewa maso Gabas a matsayin ‘yan takarar Shugabanci daga Arewa.
"Su biyun kuma za a bukaci a sake tantance su ta yadda a karshe za a gabatar da daya daga cikinsu a matsayin dan takarar da aka amince da shi, daga cikin hudun da suka gabatar da kansu daga Arewa.
Idan dai ba a manta ba, wasu jiga-jigan ‘yan takarar shugabancin kasa guda hudu a jam’iyyar PDP, sun gana, inda suka yanke shawarar takaita yawan ‘yan takarar da suka fito daga Arewacin Nijeriya, ta hanyar kulla yarjejeniya a tsakaninsu. 'Yan takarar da suka gabatar da kansu don amincewa su ne; Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Gwamna Bala Mohammed, Dr Bukola Saraki da Mohammed Hayatu-Deen.
"Haƙiƙa wannan wani babban abin a yaba ne da kuma sadaukarwa mai girma ga soyayyar ƙasa da yankin arewa musamman a ɓangaren masu neman su huɗun. Sakamakon haka, dukkannin masu neman takarar su hudu sun ziyarci tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, inda suka ba shi wa’adin jagorantar tafiyar domin cimma matsayar tsayar da dan takarar maslahar, kuma sun amince su bi sakamakon hukuncin.
A kuri'ar da dattawan suka jefa Saraki da Bala kowanensu ya samu kuri'a 10, Tambuwal ya samu kuri'a 7, sai Hayatudeen ya samu 5.