2023: Abin Da Ya Sa Ban Karbi Kujerar Mataimakin Shugaban Kasa Ba----Mukhtari Shagari 

2023: Abin Da Ya Sa Ban Karbi Kujerar Mataimakin Shugaban Kasa Ba----Mukhtari Shagari 

Tsohon mataimakin Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Mukhtar Shehu Shagari ya bada labarin yadda suka yi da mutanen Peter Obi na jam’iyyar LP kan maganar takarar mataimakin shugaban kasa. 

Da aka yi hira da shi a wani shiri na siyasa a gidan talabijin Channels, Alhaji Mukhtar Shehu Shagari yace an tuntube shi a kan maganar takara bai aminta ba. 
Tsohon Ministan yake cewa bai karbi tayin da aka yi masa na zama abokin takarar Obi a zaben shugaban kasa a karkashin LP ba saboda wasu dalilai. 
Legit.ng Hausa ta fahimci an tattauna da wasu manyan ‘yan siyasar Arewa wajen zakulo wanda zai zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a LP. 
Kamar yadda Daily Trust ta kawo rahoto, Mukhtar Shehu Shagari yana ganin babu yadda za ayi jam’iyyar LP ta doke PDP, don haka ya ki karbar tayin na su. 
Shagari wanda surukinsa ya yi shugabancin Najeriya tsakanin 1979 da 1983, ya jefawa ‘ya ‘yan LP tambayoyin da bai iya samun gamsassun amsoshi ba.