Home Siyasa Ɗan Majalisa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Ana Zargin Mutun Ukku Sun...

Ɗan Majalisa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Ana Zargin Mutun Ukku Sun Mutu Wajen Ƙaddamar Da Kamfe a Zamfara

17
0

Daga Aminu Abdullahi Gusau

Bikin kaddamar da yakin neman zabe wanda wani dan majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar tarayya ta Gusau/Tsafe, Hon. Kabiru Amadu Mai Palace ya shirya, ya haifar da tashin hankali wanda ya kai ga zargin kisan mutane uku a gundumar Mada da ke karkashin karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara a ranar Talata.

A cewar rahotanni, da muka samu, kwamitin shirya yakin neman zaben na Dan majalisar wakilai ya zabi gundumar Mada da ke karkashin karamar hukumar Gusau don Kaddamar da bikin yakin neman zabe.

A cewar wasu shaidu a gundumar ta Mada, wasu tsagerun matasa wayan da abun ya fusata su sun kawo cikas ga taron, inda suke zargin yan siyasar da rashin mayar da hankali kan batutuwan tsaro ba wai taron yakin neman zabe da aka yi niyya don ci gaba da mulki ko kuma samun nasara a kan mai rike da mukamin siyasa ba.

Danjuma Wayya, mazaunin gundumar Mada, ya ce mutane suna tsammanin ‘yan siyasa ne kawai za su kai ziyarar jaje da ta’aziyya a lokacin da aka kashe rayuka da dama a garin na Mada, aka kuma sace wasu don neman kudin fansa.

“A halin yanzu, gundumar Mada ta cika da mutanen da ‘yan fashin Daji suka kora daga ƙauyuka, don haka abin da kawai muke buƙata shi ne mu ga tallafin abinci, tufafi da magunguna daga ‘yan siyasarmu, amma ba wani mataki da ake ɗauka na neman kuri’u ba,” inji shi

Da yake ba da labarin lamarin, wani mai shago wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ba zato ba tsammani ya ga mutane suna gudu don neman mafaka, “Ban fahimci abin da ke faruwa ba, don haka na yanke shawarar kulle shagona na tafi, na tsorata lokacin da na ci karo da mutane uku suna kwance cikin jini”.

Haka dai wannan kamfen ya kare inda Jami’an tsaro na soji da Yan sanda suka bawa Dan majilisar kariya domin kauceshi ga fusatattun matasan.
Da yake wa Yan jarida bayanin, Mai magana da yawun Hon. Kabiru Amadu Mai Palace Alhaji Mustapha Gusau, ya yi watsi da ikirarin cewa matasa masu fushi a Mada sun kawo cikas ga taron, yana mai cewa, mutanen Mada sun yi maraba da bikin ƙaddamar da kamfen ɗin.

“An gudanar da taron cikin lumana da zukatan mutane cike da farin ciki saboda yawan ƙaunar da suke yi wa mai girma ɗan majalisar wakilai, Kabiru Amadu Mai Palace” ya jaddada.

An nuna rashin jin daɗin da mazauna ƙauyen suka nuna cewa, abin da mazauna ƙauyen suka fi buƙata shi ne tsaron rayukansu da kadarorinsu wanda zai sauƙaƙa musu barci da idanu biyu a rufe da kuma a cikin ɗakunansu maimakon kwana a kan bishiyoyi da kuma a cikin kogo da Kuma kan bishiyoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here