Home Siyasa Ƙungiya Ta Ƙalubalanci Yuguda Da Ya Fito Da Hujjoji Kan Zargin Tuggar...

Ƙungiya Ta Ƙalubalanci Yuguda Da Ya Fito Da Hujjoji Kan Zargin Tuggar Na Bada Cin Hancin $150,000 Don Murguɗa Zaben APC A Bauchi

10
0

Daga Khalid Idris Doya.

Wata ƙungiyar magoya ‘Tuggar Vanguard’ ta musanta zarge-zargen da tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda, ya yi na cewa ministan harƙoƙin wajen Nijeriya, Amb. Yusuf Maitama Tuggar, ya bayar da cin hanci na dala $150,000 domin jan ra’ayi wajen ganin an bi ko zaɓan son ran ministan yayin zaɓukan shugabannin jam’iyyar APC a jihar Bauchi.

A cikin wata sanarwar manema labarai da ƙungiyar ta fitar a jiya wanda shugabanta, Garba Mohammed, ya sanya wa hannu, ya bayyana cewar irin su waɗannan zarge-zargen suna da matuƙar girma don haka dole a fito da hujjoji domin tabbata da zargin da ake yi.

Ya ce su na martani ne kan rahoton da ke cewa ministan ya bayar da kuɗaɗen ne domin rinjayar rahoton zaɓukan jam’iyyar APC a jihar Bauchi tare da sauya su zuwa yadda ya ke so.

Ya ce wannan zargi ne mai girma wanda ke buƙatar ingantacciyar hujja. “A kowace al’umma mai bin doka, ba za a jingina zargin cin hanci kan zato, jita-jita ko fushin siyasa ba. Dole ne ya zama akwai ƙwararan hujjoji da za a gabatar. Don haka muna ƙalubalantar Isa Yuguda da ya fito da hujjojinsa duniya ta gani.

“Idan akwai hujja, ya kamata a gabatar da ita ga hukumomin da suka dace. Kafin a gabatar da hujjojin za mu ɗauƙi batun a matsayin zargi har sai an tabbatar wa duniya. Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda Yuguda ke zubar da mutuncinsa da irin waɗannan zarge-zargen mara tushe balle makama.”

“Jihar Bauchi na buƙatar sauyi na haƙiƙa, ba tsohuwar ƙiyayya ba, ko wasan kwaikwayon siyasa da zarge-zargen da ba su da hujja daga waɗanda ke ganin mulki tamkar gadonsu ne,” ƙungiyar ta shaida.

Garba ya kuma yi gargaɗin cewa irin waɗannan zarge-zarge marasa tushe na iya ɓata sunan mai yin su, yana mai cewa irin kalaman suna fi ɓata kimar mai zargi fiye da wanda ake zargi.

Ƙungiyar ta kuma ƙaryata cewa Yuguda ne ya taimaka wajen tasowar Tuggar a siyasa, tana mai cewa Ministan ya lashe zaɓen ɗan majalisar mazabar Gamawa a 2007 ne bisa cancantarsa da goyon bayan jama’a.

“A lokacin, Yuguda yana cikin rikice-rikicen siyasarsa a Bauchi wanda wannan rikicin shi ne ya ja hankalinsa, kuma nasarar Tuggar ba ta dogara da shi ko tasirinsa ba,” ƙungiyar ta yi iƙirari.

Dangane da zargin cewa Tuggar na haddasa rikici a APC a Bauchi, Mohammed ya ce Ministan ya nuna jajircewa da aminci a harƙar siyasa tun daga ANPP, zuwa tafiyar Buhari, zuwa CPC, sannan APC.

“Ba a san shi da yawan sauya sheƙar siyasa ba. Amma tarihin Yuguda ya nuna sauya jam’iyya a fili, wanda har yanzu jama’a ke tunawa da shi. Wannan ya sa zarge-zargen da yake yi kan daidaiton jam’iyya suke buƙatar a duba su sosai,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa Isa Yuguda na daga cikin ‘yan APC kaɗan da ke sukar sakamakon zaɓukan cikin gida, domin sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar ba su fito fili suna goyon bayan wannan matsayi ba.

Ƙungiyar ta buƙaci ‘yan jam’iyya masu koke da su bi hanyoyin cikin gida na warware matsaloli maimakon yin zarge-zarge a bainar jama’a wanda zai iya tayar da hankali.

Mohammed ya jaddada cewa siyasar Bauchi bai kamata ta zama ta koke-koken wasu tsiraru ba, yana mai cewa ci gaban jihar ya fi muhimmanci a kan muradun ƙashin-kai.

“Abin da jihar ke buƙata a wannan lokaci mai muhimmanci shi ne shugabanci nagari, mu’amala mai tsari da kuma cikakken jajircewa wajen ci gaba. Mutanen Bauchi na buƙatar siyasar da za ta ciyar da jihar gaba, ba wadda za ta mayar da ita baya cikin rarrabuwar kai da koma baya ba.”

“Daga cikin ɗimbin jiga-jigan APC a Bauchi, Yuguda na daga cikin kaɗan da ke fitowa fili suna sukar sakamakon zaɓukan cikin gida,” Garba ya shaida.

Ya ci gaba da cewa jam’iyyar na da tsoffin gwamnoni, sanatoci na baya da na yanzu, ‘yan majalisar wakilai, ‘yan majalisar dokokin jiha, tsoffin ministoci da sauran manyan jiga-jigai, kuma rashin goyon bayansu ga matsayar Yuguda na sanya ayar tambayar anya kuwa koke-kokensa ke wakiltar ra’ayin jam’iyya ne ko ta ƙashin kansa.

A ƙarshe, Garba Mohammed ya yi kira ga ‘yan siyasa da su mayar da hankali kan matsalolin jama’a tare da bin manufar “Renewed Hope Agenda” ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman wajen mayar da Bauchi cibiyar noma da haɓaka albarkatun ƙasa, ba wai biye wa rikicin cikin gida ta hanyar son ran wasu tsiraru ba.

“Wannan shi ne babban ƙalubale da kuma dama. A nan ne ya kamata shugabanni masu hangen nesa su karkata hankalinsu,” in ji Mohammed.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here