Home Siyasa Ɗan takarar Gwamna ya ajiye takarar sa ya koma APC a Sokoto

Ɗan takarar Gwamna ya ajiye takarar sa ya koma APC a Sokoto

7
0

Kwana ɗaya kamin soma yekuwar zaɓen gwamna a kakar zaɓen 2027 kamar yadda hukumar zaɓe ta tsara ɗan takarar Gwamna a jam’iyyar Labour(LP) Honarabul Aminu Ahmad Umar da aka fi sani da Maxia ya jingine takarar da yake yi ya kuma bar jam’iyyar zuwa APC.

Aminu Muhammad ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da waƙilinmu a Sakkwato ya ce yabar jam’iyyar LP ne zuwa APC domin taimakawa a gina al’ummar jihar Sakkwato a yanzu akawai buƙatar a shiga cikin jama’a domin yin harkokin siyasa.

“In ka duba siyasa a yau tana buƙatar al’umma da kuɗin gudanar da ita, ƙananan jam’iyyu ba su da wannan damar sai na yi la’akari da lokaci baya gefe na akwai buƙatar na koma in da zan iya ba da tawa gudunmuwa domin samun sauyi wasu abubuwa da dama, duk yanda abubuwa suka yi tsanani da jajircewar shugabanni da mutanen ƙasa za a samu sauƙi, matakan da ake ɗauka a ƙarshe ‘yan Nijeriya za su ga fa’idar lamarin, suna cikin abin da ya ƙara ƙarfin guiwar na shigo don ba da tawa gudunmuwa.”

“In ka duba talakawa wata jam’iyya suka canja suka kawo APC da tunanin ta kasa matuƙar talakawa ba su tsaftace siyasa ba suka daina karɓar ɗan abinda bai taka kara ya karya ba, don su yi zaɓe; su sani ba matsalar shugabanni ba ce har da mu al’umma, in ba a gyara ba mafita za ta yi wuyar samuwa,” a cewar Aminu Ahmad.

Ya ce da zaran talakawa suka riƙa yin abin da ya dace za a samu yanda ake so a shugabanci, su daina karɓar kuɗi don yin zaɓe, ka ji mutum na cewa ko bai amsa ba ci za a yi in ji wa, yakamata kuma yanzu a faɗawa gwamnati gaskiya ina ‘yan majalisun da muka zaɓa da gwamnoni ba su jin koken da al’umma ke yi, muna fatan wannan gwamnati za ta samar da abubuwan da ake buƙata, “ban gamsu da a samar da sauyin gwamnati ba, don waɗanda ke son su sauya gwanati an ba su dama ba su yi abin a zo a gani ba, kuma matakan da gwamnati mai ci ke ɗauka zai amfani talaka a gaba, za mu ba da tamu gudunmuwa a tsare-tsaren gwamnati don kai ga nasara,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here