Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta Huɗu

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta Huɗu

9
0

©AUNTY NICE

🔘ƘADDARA TA RIGA FATA🔘

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 4

__📖 Ina zuwa ƙofan shi na tsaya ina murmushin gudun da nayi, a zuciya ta nace “hala shima ya razana ne yasa ya tafi ya barni a wurin ko kuma shima tunanin shi iri ɗaya ne da Yaya Ahmad ɗin mu, don shi kullum cewa yake al’janu nake da shi shiya sa nake yawan jin tsoro”,
tunanin haka ni kaɗai sai ya sakani dariya domin tunawa da nayi wata rana bayan Yayan mu ya gama mun faɗa akan yawan jin tsoro na, na juya zan tafi ɗaki fuskana a ɗaure kawai sai naji ihun shi ya tashi da gudu yayi ɗakin Maman su.

Nima bayan shi nabi da gudu har ɗakin Maman, sai naji yana cewa Maman, “Gatanan ma sun sakata ta biyo ni, don Allah Mama ki koreta a ɗakin nan wallahi ina mata faɗa sai naji wani abu yabi ta ƙafana ya wuce mai shegen laushi”.

yana faɗa duk zufa ta jiƙa fuskan shi.

Da tsawa Mama ta mun magana akan na fita na bata wuri da shegen ido na irin na mayu, cikin sauri na fito ,ina zuwa parlor sai ido na ya sauƙa akan ƴar kyanwata da ɗazu na same ta a wurin Baba maigadin mu, dariya ne ya so suɓuce mun don sai yanzu na gane abinda yabi ƙafan Yaya Ahmad wato wannan ƴar magen ne yaji laushin jikin ta a kan ƙafar shi, shi kuma yayi tunanin jinnu ne, ina ƴar munafukar dariya naje na ɗauketa na fita da sauri zuwa wurin Baba maigadi, miƙa mishi magen nayi a hankali nace,

“Baba ɓoye mun ita anjima zan kawo maka madaranta da kuɗin ƙosai idan Daddy nah ya sauƙo, yanzu idan Yaya Ahmad ya gani zai mun jifa da ita don yana tsoron mage”.

na faɗa ina komowa cikin gida da sauri na.

Ina tsaye a bakin ƙofan Dr Hussain ina ta dariyan abinda ya faru sai kawai naga ya buɗe ƙofan yana kallo na,

Da sauri na saka hannu na na rufe bakina ina maida dariya na, ido na cikin na shi nace,

“Dr mu kaima kaji tsoron ko ina da al’janu ne yasa ka gudu ko? Kasan a gidan mu Yaya na Ahmad bai taɓa yadda cewa bani da al’janu ba tsabar tsoron shi, kaima kana tsoro ne?”.
Na faɗa ina mishi dariya.

Hasbunallahu wa ni’imal wakil ya faɗa cikin zuciyar shi, bayan ya ƙura mun ido, ganin abinda na faɗa ya sake tuna mishi cewa wataran fa AISHA ta taɓa faɗin irin wannan kalman, nacewa ko yana mata kallon mai jinnu ne?, runtse idon shi yayi har zuwa wani lokaci, kaman ba zai buɗe ba amma sai ya sake jin muryana ina cewa.

“Dr mu don Allah kayi haƙuri ka bani phone ɗina zan gaishe da Daddy ne, kuma ina tsoron ya ƙira yaji shi a hannun wani kaga ba zai ji daɗi ba, kasan Daddy ya damu da rayuwa ta, kullum yana cemun na nisanci tarayya da maza saboda basu da amana, kaga idan yaji yana hannun ka zai ce amma yarinyar nan ƴar kawai ce, ita dana turo ta karatu me ya haɗata da maza? Bai san kuma kai ɗin ba maza bane kai Dr mu ne ba zaka cuce ni ba ko?”.

na faɗa ina turo kaina gaba irin ina jiran ya bani amsa.

Zuciyar shi ce ta sake yankewa, domin tunawa da irin wannan kalaman daya taɓa ji a wurin Aisha, kuma tsarin maganan Aisha ne cewa, “Yaya Hussain ɗin mu”.

komai zata faɗa mishi sai ta dangana shi da shi nasu ne, kuma Aisha ce mace a duniya daya taɓa ganin idan bawai mutum ya cuce ta bane tou bata taɓa ƙin yarda da shi, ita kullum tunaninta zuciyar kowa mai kyau ne, saboda haka ita duk macuci sai ya nuna kaman shi take ganewa, tou yau ga wata Aishan a gaban shi irin Aishan su tana mishi irin maganan ta, da kuma nuna mishi yarda a lokaci ɗaya.

Hawayen da yake ɓoye wane suka gangaro mishi, amma gudun kada wannan yarinyar mai surutun tace yana kuka a gaban ta sai yayi sauri ya saka hannun shi a al’jihun wandon shi ya fito da phone ɗin ya miƙa mata.

Zuba mishi ido nayi cikin alamun rashin jin daɗin yanayin dana ganshi a ciki, a hankali na ɗan matso kusa da shi a hankali nace,
“ka tuna da Maman kane?”.

Sai kuma na ɗan leƙa cikin parlon da kaina, kaman ina neman wani abu, a hankali na dawo da kaina waje cikin ƙasa-ƙasa da murya nace,
“Kunyi faɗa da matar kane? Bata maka abinci bane?”.

Ina kallon shi idona duk a waje domin jiran me zaice mun.

Babu shiri naga yayi murmushi kaɗan, kuma sai ya maida fuskar shi irin tada, baice mun komai ba naga yamayar da ƙofan ya rufe shi kuma yana shirin zuwa jikin motar shi domin ya fita a compound ɗin gaba ki ɗaya.

Gudu-gudu na ƙarasa inda yake, kaman zan riga shi shiga cikin motan, ganin haka ya saka shi tsayawa yana kallo na cikin mamaki, ni kuma ɗan murmushi nayi sannan nace.

“Dr’n mu hala zaka tafi weeƙend wurin wife ɗinka da yaran kane ko? To meyasa su basu zuwa maka sai dai kullum kai kaje? Ko kuma kaine kafi son zuwa ita bata so?”.

Shi dai kallo na kawai ya keyi cike da mamaki na, bai iya yace mun komai ba sai ido daya ƙura mun, murmushi na sake mishi sannan na cigaba da magana na, wanda ko kulawa da rashin bani amsan da yayi tun fitowar shi banyi ba, nace

“Dr’n mu to ka kawo mun yaran ka mana, kaga Daddy ya hanani yawo da naje na gan su, kuma na gajji da zaman shiru ni ɗayan nan”.
na faɗa ina ya mutsa fuskana alaman har zuciya ta zaman ya ishe ni.

“AISHA ki koma kije ki ƙira Daddyn ki, ni kuma plz ki bar ni na fita akwai abinda zanyi”.
kaman daga sama naji muryan shi yana faɗa mun haka.

Matsawa nayi har ya shiga motan ya zauna, ni kuma hannu na yana riƙe da marfin motan, cikin shagwaɓa nace, “Dr’n mu yaushe to zaka dawo? Don Allah ka dawo yau, ni nafi soma ka dawo da su nan na dinga ganin mutanen da zan dinga hira da su”.

“Hira aka kawo ki kiyi ko karatu?”.
Ya faɗa yana rufe ƙofan shi, ina kallon shi bai sake cewa komai ba har ya fita da motan shi, na buɗe baki na zanyi magana kawai naji ƙiran Daddy na yana shigowa, da sauri na koma nawa side ɗin domin na nutsu muyi hira da Daddy na.

Duk zuba idon da nayi ganin Dr ya dawo yau amma shiru har dare bai dawo ba, ina zaune ni kaɗai na naja tsaki sannan nace,
“hala a wurin su zai kwana, to shi in banda shiririta meye na raba gida da matar ka? Kawai ka dawo ku zauna a wuri ɗaya ai ina ga zai fi bada ma’ana”.
a zuciya ta nake faɗin hakan, can kuma na faɗa murya a bayyane nace,

“Nikam ni Humaira bazan taɓa yadda na raba gida da miji na ba, duk in da yake to nima a wurin nake”.

ni ka ɗai sai na bawa kaina dariya ni da bani da ko saurayi mai ya kaini ma tunanin wani miji kuma? To idan ma zanyi auren wani irin miji nake so? Kuma ya ya irin tsarin mijin dana ke so zai zama, rufe idona nayi ina wassafa ya ya tsarin shi da kamanni shi yake.

Nifa ina son miji fari, ina son miji dogo kaman (Nuhu Arabi) marigayi, to amma kuma ina son miji mai son ado da kuma son saka turare, to ya ya zai kasan ce kamanin shi?………

Da sauri na tashi daga jingunuwan da nayi domin gaba ɗaya sai naga yanayin Dr nake so, kuma kamanni shi ne suka bayyana mun a zuciyar tunani na, baki na buɗe nace,

“Dr kuma ai ya girma da yawa, don daga ganin shi yana da ɗa ko ƴar da ta kai 10yrs, kai haba ba zai yiwu ba, wannan daga gani mata ɗaya ta ishe shi don tsarin shi duk na turawa ne”.

na faɗa ina kuma kwanciya ta a kan kujeran parlon.

Agogon ƙasar ya nuna 10:00pm, ni kuma dai-dai lokacin na fito a wanka, rigan bacci iya gwaiwa na nasa ka, sannan na shafe jiki na da turaren Humrah da na taho da shi, hula na mai kama da net na saka, ina cikin gyara gado na wanda ya bi jiki na dole idan zan kwanta sai na sake gyarawa, a lokacin naji an buɗe gate ɗin gidan, kuma naji ana shigowa da mota, da sauri naje na leƙa ta window kawai sai naji dariya ya suɓuce mun ganin Dr ne ya dawo, kaman wani ɗan’uwa na naji zuciya ta ta yi haske.

Da gudu na fito a ɗakin nayi hanyar waje, ina buɗe ƙofa na shi kuma yana rufe motan shi, hannun shi riƙe da wani leda mai ɗan girma, banyi shiri ba kuma banyi shawara da zuciya ta ba, kawai na samu kaina da zuwa da gudu na saka hannu zan karɓi ledan hannun shi, fuska na cike da farin ciki ina faɗin,

“oyoyo Dr’n mu, dama jiki na ya bani yau kam zaka dawo, ba zaka kwana a can ba, ka taho da ƴaƴan ka ne?”.

Na faɗa ina leƙa bayan motan.

Ina tunanin ya sake mun ledan, amma sai na ji ya ƙi sakewa, da sauri na dawo da fuska na kan ta shi fuskar nace,

“Dr’n mu ka bari na ɗauka maka mana, kasan na kasa bacci ina ta tunanin zaka dawo ko ba zaka dawo ba? Kasan ban ci abinci bama saboda tunanin ba zaka dawo ba, yanzu kuma ka ƙi yarda na ɗauka maka kaya? Haba Dr’n mu”.

na faɗa cikin sakalci da muryan kuka.

Sai ji nayi ya sake mun ledan a hannu na, ni kuma da sauri na ƙarasa na shi ƙofan, wanda muke jere da shi, kuma namu yana kallon na waƴan can, ina tsaye ya ƙaraso har in da nake, baice mun komai ba ya saka key ya buɗe ƙofan ya miƙa mun hannu alaman na bashi ledan.

Ido na zuba mishi alaman ya barni na wuce mishi da shi ciki, runtse idon shi yayi ya buɗe ya sauke akan nawa, kaman bazai ce uffan ba, sai kuma ya dube ni sama da ƙasa sannan yace,

“Dubi irin shigan da kika yi Aisha? Ba kiji Daddy’n ki yace kada ki shigewa maza ba domin zasu iya cutar dake? To ke baki jin maganan Daddy’n kine ko kuma sakacin daga kece? Baki tunanin ni na cutar dake? Duk da kince ni ba namiji bane ba ko?”.

Ya faɗa yana ɗan buɗe mun idon shi a kaina.

Turo mishi baki na nayi gaba kaman zanyi kuka, ina kallon shi nace ai samari ne suke cutan mata ko ƴan matan su, kai kuma ai Malamin mune idan babu idon iyayen mu ai kune iyayen mu ko? Kaga kenan kai ba zaka cuce ni ba, kuma zaka ga ai kaman ni ƴar kace tun da ban riga dana zama budurwa ba, 16yrs fa nake, kasan Daddy da wuri ya saka ni school”.

na faɗa ina langaɓar mishi da kaina.

Baice mun komai ba ya juya ya shige parlon, da sauri ni kuma na bishi a baya hannu na ɗauke da ledan, wanda gaba ɗaya nauyi yamun, muna shiga nayi karo da wani daddaɗan ƙamshi mai masifar tafiya da tunanin mutum, ajiye ledan nayi ina lumshe ido, ina buɗewa muka haɗa ido da shi, ya ƙura mun ido yana kallon yadda nake nuna jin daɗi na akan ƙamshin da naji.

“Yaya Hussain kai fa ɗakin ka idan mutum ya shigo sai yaji kamar kanshi zai kunce tsabar daɗin ƙamshin da yake yi, ni wallahi duk duniya ban taɓa ganin ma’abocin son ƙamshi ba irin ka, motan ka ya kama ƙamshi, kai kanka ƙamshine sunan ka, ɗakin ka kuma kaman shine company turare”.

muryan Aisha ya tuno wani lokaci yace ta dafa mishi indomie ta kawo mishi ɗakin shi yaji a kunnen shi kaman yanzu abun yake faruwa.

Buɗe ido nayi ina duban yadda ya runtse idon shi, abin sai ya ɗaure mun kai, matsowa nayi kusa dashi na kira sunan shi a hankali, “Dr Hussain”.

A razane ya buɗe idon shi ya kalle ni, sannan a zuciyar shi yace wannan hatta muryan da yadda Aisha ke kiran sunan shi irin nata ne.

wuri ya nema ya zauna bai kalle ni ba yace,
“nagode ki tafi kije ki kwanta dare yayi”.
yana faɗa ya komar da kanshi ya kwantar a saman kujeran da yake zaune yana runtse idon shi.

“Dr gobe nayi breakfast da kai? Kana son cin ƙosai da kunun gyaɗa? Kasan ina da abin markaɗa wake, kuma last week ma nayi kunun gyaɗa na saka mishi milk yayi daɗi irin wanda ba a bawa yaro mai ƙiwuya tahm! tahm!! tohm!!!”.
na faɗa ina jijjiga kaina alaman idan yayi wargi bazan bashi ba.

Ƙura mun ido yayi ya sake faɗi a cikin zuciyar shi wannan kam ko dai Aisha ce su Abba suka turo ta wuri na? Don daga Ummin shi sai Aisha suka fi kowa sanin abinda yafi so da irin girkin da yafi so, to idan ba Aisha bace ya ya aka yi tasan yana son ƙosai da kunun gyaɗa kuma a saka milk a ciki?.

“AISHA Abba ne da Ummi na suka ce kizo nan ki same ni? Sunce miki idan kinzo ki gaya musu ina nan ne?”.
Ya faɗa idon shi a kaina.

A hankali na tako har inda yake na zauna a hannun kujeran da yake, ina duban shi a nutse nace,

“Daddy na bai san ka ba, amma yace mun a kwai wasu a gidan da kake, saboda lokacin da ya kama gidan ance mishi dama saura na mutum ɗaya ne, amma bai san ka ba, kuma da ya san ka daya gaya mun don ba ya ɓoye mini komai”.

na faɗa ina maida fuska na kaman zanyi kuka, don ganin yadda hankalin shi ya ta shi.

“Don Allah kije ki kwanta nima kwanciya zanyi”.
ya faɗa mun ba tare da ya buɗe idon shi ba.

Tashi nayi tsaye ina gyara ɗan riga na sannan nace, “don Allah nayi breakfast ɗin da kai”?

Jijjiga kanshi yayi alamar eh.

“What time kake ta shi saboda nasan time ɗin da zan yi so that kada ƙosan ya yi sanyi, kasan shi idan yayi sanyi baya daɗi, kuma idan an saka shi a cooler zufa ya keyi, baza kaji daɗi ba, shida indomie halin su ɗaya, kawai kyan su ana yi aci a lokacin”.

“Ya Rabbi”.
ya sake faɗa a fili bayan ya sauƙe idon shi a kaina, wanda zuciyar ji yake kaman zata ɓalle ta fito tsabar al’ajabin abinda yake faruwa.

Ganin nayi hanyar waje da sauri ya buɗe bakin shi yace, “10:00am is okay”.
ka ɗa mi shi kai kawai na yi na buɗe ƙofan na fita.

Ni Aunty Nice to meye wannan ruɗanin da yake damun Dr Hussain? na tambayi Miss Zerks da muke bin bayan Humaira, ita ma duba na tayi cikin mamaki ta ce ni fa Aunty Nice abin yana ɗaure mun kai, don kawai kada kiyi fushi ki kore ni ne kawai yasa ban tambayi Dr Hussain ɗin me yake faruwa ba.

tsayawa nayi da tambayan nawa nayi ina kallon ta nace, “ko tayi kama ne da Aishan?”.

watsa hannun ta tayi alaman bata sani ba, sannan ta ce, “nidai Aunty Nice zan tambaye shi, amma don Allah kada ran ki ya ɓaci, haba hankalina duk yana kan nasan me yake faruwa”.

hararanta nayi da sauri tace, “Na fasa to”.

_Plsss and Plsss comment kunji mutanen kir ki

AUNTY NICE 😘✍🏻

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here