Home Daga Marubutanmu Ƙaddara Ta Riga Fata: Fita Ta 24

Ƙaddara Ta Riga Fata: Fita Ta 24

7
0

AUNTY NICE✍🏼*
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 24📑

__📖 2dys da zuwan mu DAMMAM Faisal ya iso, kai masha Allah wato Faisal ya ninka Amaal kyau sau babu adadi, ga wani class a tattare da shi, lokacin da na fito parlor inda suke ta murnan ganin shi tsayawa nayi ina kallon inda yake bakina ɗauke da murmushi, Amaal ce ta nuna mishi ni tana dariya tace, “Humairah” da sauri ya juyo inda nake ya ƙura mun ido yana murmushi shima.

Ganin haka ya saka ni takowa zuwa inda suke cikin tafiyata kaman na tarwaɗa tsaban yauƙi daya mun yawa, wani ɗan sautin dariya ne marar ƙarfi ya ɗan suɓuce mishi a bakin shi, a hankali ya furta, “woow beautifull” sannan ya juya ya kalli Ummi yana murmushi yace, “Kai Ummi yarinyar tana da kyau da yanga, Ummi ina son yanga a wurin mace” hararan shi Ummi tayi tace, “Hummy sister ka ce fa, don haka bana son fitina”.

Ina ƙarasowa na mishi sallama har lokacin bakina ɗauke da murmushi, da sauri ya kamo hannu na ya jawo ni jikin shi ya rungume ni irin yadda suke gaisuwan su, sannan ya sumbaci kuncina, ba karamin faɗuwar gaba naji ba don gaskiya ni ba’a taɓa mun haka ba, gara ma Abbu da safe haka yake mana amma bana jin komai saboda shi ae uba ne, amma wannan gantsamemen saurayin fah? Ga wani ƙamshi da yake tashi a jikinshi kaman wani amaryah, cikin ƙarfin hali nake gaisheshi saboda har lokacin bai sake ni ba saidai ya ɗago ni daga jikinshi yana riƙe da kafaɗa na duka biyun, ga wani murmushi mai masifan kyau a fuskan shi.

Ya kamata naji haushin abinda yamun amma sai naji na kasa saboda wani irin kyau da kwarjini da ya mun, ga shi mai tsafta ɗan gayu, ina murmushi na saka hannu na ina cire nashi da yake kafaɗa na, a hanakali yace, “kina da masifan kyau Hummy, kyaun ki mai kyau ne” gabana naji ya faɗi, gaskiya Faisal ya haɗu duk da bai kai Dr nah kyau ba, amma yau ɗaya yamun abinda Dr na ya kasa yimun kusan 4month, yau kalman da nake so naji a na yawan furta mun ni mai kyauce Faisal ya furta mun har yana wani kashe mun ido.

Wucewa nayi inda Ummi ta ke zaune na zauna a gefenta , har zuwa lokacin fuskana ɗauke da murmushi, domin haka kawai Faisal ya sauƙe mun wani nishaɗi a zuciyata, gaskiya ni Humairah me kyauce, amma haka kawai nake jin son kyawawan mutane, don bana mantawa idan kakata wadda ta haifi Mamana idan tazo duk inda tayi na dinga kallonta kenan, domin ba ƙaramin kyau takeyi mun ba, gata da gashi mai tsawon gaske, bana gajjiya da kallonta, haka ita kanta Amaal bana gajjiya da ganinta domin kyau ta keyi mun, yau ɗaya naga Faisal yafi mun Amaal kyau, gashi shima yana yaba nawa kyaun.

Da sauri na ɗaga kaina domin jin abinda Faisal yake gayawa Amaal, “sister dama haka Hummy ta ke da kyau shi ne baki taɓa nuna mun ita ba? bayan na biki ko a photo ne ki nuna mun ita amma kinƙi, ashe mai kyau aka ɓoye mun? gaskiya gara da nazo na ganta da kaina”, ya juya wurin Ummi yana murmushi ya dafa cinyan ta yana magana cikin shagwaɓa, “gaskiya ni Ummi ina son Hummy na gaskiya bana wasa ba, gaskiya Ummi nikan dani ta dace, ko ajiye mun ita na kusa gama karatuna”, ya faɗa yana kwantar da kanshi kan cinyan Ummi, idon shi kuma duk ya sauƙe mun su, sai wani kashe mun ido kawai ya keyi da zaran mun haɗa ido, nidai kunyan shi kawai nakeji, sai wani smilling mai ɗauke hankali na ke tayi.

“Baka isa ba wallahi bros Faisal, ta yayah ma zanyi wa Dr Hussain haka? gaskiya toh wasan ma ya isa haka, bayan Hummy da Dr sun amincewa junan su, gaskiya kabar maganan nan bazai taɓa faruwa ba”, ta faɗa tana miƙewa tsaye, idon ta akan Ummi tace “Ummi ki gaya mishi gaskiya ya dai na irin haka, ni bazai saka naji kunyan Dr ba”, sannan ta kamo hannu na tace, “mu tafi ɗaki hummy”.

Miƙewa yayi shi ma yana hararanta yace, “wallahi sis baki isa ba, kinsan haka ta ke shi ne zaki wani sako ni acikin shirmenki, toh ni ma ae namiji ne saidai kowa ya gwada jarumtar shi, wanda yayi nasara Humairah ta zama rabon shi, kuma kibar yarinya ta zauna a inda ya mata bawai ki kai ta bedroom ki kulleta ba”, ya ƙarasa faɗin maganan yana kamo hannu na, da sauri na juyo na dubi Ummi da ta zuba mana dukkan idonta akan mu bakinta a buɗe, maida kallo na nayi kan shi amma da sauri na kawar da kaina ina ƙoƙarin ƙwace hannu na, domin ni ban san me nake gani a cikin idon shi ba, gashi bana son ya riƙe ni amma kuma bani da ƙarfin gwiwan hana shi, narai-narai nayi da ido alaman zan mishi kuka domin nakasa ƙwace hannu na.

Sun kuyawa yayi dai-dai kunne na yace, “kada ki tafi da bugun zuciyata ya ke ma’abociyar kyau na duniya, nafi son na dinga ganin kyakkyawan idon ki da ɗan ƙaramin bakin ki mai matuƙar tafiya da hankalina a kusa dani ya mai kyau”, wayyo Allah jina nayi numfashi na yana shirin tafiya lokaci ɗaya, abin na kwace hannuna daga nashi sai na samu kaina da ƙara damƙe hannun shi cikin nawa, wanda bansan dalilina nayin hakan ba.

Ganin haka ya saka Ummi miƙewa da sauri tace, “sakar mata hannu fav, baka san abunda kake yi mata ya saɓawa shari’an musulunci ba, ko ce maka akayi hannun Amaal kake rike da shi? bana son sakarci, sake mata hannunta ta bi ƴar’uwarta”.

Da sauri ya sa ke mun hannu yana sauƙe numfashi kaman wanda yayi gudu, ya juya yana kallon Ummi cike da shagwaɓa yace, “haba mana Ummi!! nifa wallahi bazan cutar da ita ba, kawai ki gane Ummi sonta fah na keyi over”, bayan ya saka hannu yana wani dafa ƙirjin shi kaman wanda yake jin wani ciwo a wurin.

Hararan shi cikin so da ƙauna Ummi tayi, sannan ta buɗe mishi hannu alaman ya taho gareta, da sauri yaje ta rungume shi ta wani bubbuga mishi bayan shi kaman wani yaro ƙarami, murya ƙasa-ƙasa ta ke rarrashin shi, “haba fav kasan fa Humairah amana ce a wurin mu, yayah karon farko zaka fara riƙe mata hannu kana jawota jikin ka? Kuma kasan akwai wanda sukayi alƙawarin aure kuma ya maida mu kaman iyayen shi, ae bai kamata mu baka daman ka so ta ba, saboda bazai ji daɗi ba kuma bazai yadda damu ba a gaba, kayi haƙuri farin cikina Allah zai baka wacce tafi Humairah insha Allahu”.

bamu jira munji mai zai ce ba Amaal ta jawo hannuna da sauri muka wuce ɗakinta, muna shiga ta fara masifa kaman zata mare ni, “haba Hummy ki zama very careful da ɗan’uwa na domin kada ki bari yaje ya ɗauke hankalinki akan Dr, don wallahi Dr bazai taɓa yafe miki ba, kuma nima zaki sakani jin kunyan shi, don wallahi tsab Faisal zai gama da zuciyar ki acikin kwanaki kaɗan”, ta faɗa tana hararana.

   Murmushi nayi ina duban ta, a hankali na zauna a kusa da ita na saka hannu na riƙo nata hannun nace, "nikan Amaal kibar tunanin akwai abinda zai ɗauke hankali na akan Dr, ni ina yiwa Dr son da ban taɓa tunanin wata mace tana yiwa wani ɗa namiji ba, kai ko tunanin wani zai ɗauke hankali na akan Dr bana yi, saboda haka ki kwantar da hankali ki besty nah", na faɗa ina bin ta da murmushi.

“Hmmm bazaki fahimta bane, wallahi bros Faisal tsab zai ɗauke hankalin ki domin yasan yadda zai nuna miki kulawan da baxaki iya tunawa da wani ba bayan shi, nifa ɗan’uwa nane kuma nasan halinshi akan abinda yaga yana so, don ko abu yake so a mishi yasan yadda zai ɗauke hankalin su Ummi da Abbu su mishi babu shiri, kedai ki maida hankali kawai, bana son kina bashi haɗin kai ko yazo inda kike kinji”, ta faɗa tana duban cikin ido na.

“Ashe baki sona da alkhairi ko ƴar’uwata? wato kin fi son farin ciki wani bari akaina ko Amaal? toh bana so ki zugata kibarta tayi amfani danata ra’ayin ta zaɓi wanda yayi mata bawai sai kin mata shishshigi ba”, …..Faisal ya faɗa ya na tahowa inda muke shima ya zauna a kusa dani, sannan ya dawo da hankalin shi kaina.

Yana murmushi ya saka hannun shi ya riƙo nawa, ido na nayi saurin buɗe su a kanshi, amma sai na kasa ce mishi uffan domin yadda naga ya runtse idon shi bayan ya riƙe dukkan hannuna yana ta matsa mun yatsuna a hankali a hanakali, da sauri na dubi Amaal da ta buɗe baki tana kallon ɗan’uwanta.

“Mine kice mun wani abu mana da daddaɗan muryanki hankalina ya kwanta”, yana wani langwaɓe mun kaman mai yaron da yake shirin shan nono, murmushi nayi na ɗaga idona ina kallon shi, a hankali na buɗe bakina nace.

Toh ina team Dr, ku fito kada Faisal ya ƙwace muku Hummy, don jikina ya fara sanyi da al’amarin Faisal, amma bari mujira muji yyh zata kaya a tsakanin su

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here