Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 44

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 44

15
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NIC
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 44📑

__________📖 Aisha tana da 14yrs muka gama karatun mu muka dawo service a ƙasar mu, babu ɓata lokaci muka taho bauchi wurin parent ɗin mu muka fara service ɗinmu hankali kwance, shekara babu wuya haka tazo har muka shekara guda muka gama.

Muna da 22yrs muka dawo gida kowan mu ɗauke da masters ɗinshi, shekaran kuma Aisha ta gama secondry sechool da 1yr kenan, lokacin tana da 17yrs, mundawo Aisha ta samu admission a ATBU, inda zata karanta micro biology, tunda muka dawo Hassan tsamarsu da Aisha ya yi yawan gaske, babu hali ta zauna zakaji ya fara cewa ita da ba’a sonta an barta karatu a nija, haka zatayi ta kuka tana cewa Abba ita ma, dole saidai a fitar da ita waje, amma Abba sai yayita rarrashinta akan tayi haƙuri tayi a gabanshi, da ƙyar zata huce, ni kuma haka kawai na samu kaina da rashin yawan magana, idan har kaji bakina toh Ummi ne ko Abba na, amma Aisha kuma kaman ance ta dinga shige mun, ni kuma ina jan jiki da ita saboda ita ƙanwatace, amma kuma sai wani baƙon Al’AMARI yana faruwa dani, babu hali na kwanta sai nayi mafarkinta, kuma duk inda zanga budurwa ko ta nuna mun tanayina, babu wacce zata zo mine ɗine sai Aisha, watarana muna kwance da Hussain a parlourn mu nida shi, da yake side ɗinmu parlour ne da 2bedroom, inda ina amfani da ɗaya shima yana amfani da ɗayan, ina kwance na ɗaura dukkan hannuna na rufe idona kaman mai bacci, kawai saiga Aisha da mugun gudu ta shigo parlourn mu, saɓye da wani shegen wando da ɗan figigin riga a jikinta, sai wani ƙamshin daɗi ta keyi, kawai jin mutum nayi ya faɗo jikina.

A razane na miƙe zaune, wanda dole ta ɗago itama ta biyo jikina muka tashi zaune tana rungume da ni, gaba ɗaya notin kaina saida suka neme kuncewa, saboda Aisha yarinyace wanda chest ɗinta yake cike da breast masu masifar girma da ɗaukan hankali, duk yadda naso tureta kasawa nayi, kawai ƙura mata ido nayi ina kallon bakinta yadda take ƙyalƙyala dariya tana duban idona.

Ganin yadda nakasa ta ɓuka komai yasa Hassan ya daka mata tsawa yace, “ke kam mahaukaciyar ina ne da zaki rungume mutum ne wai? Don Allah ki ɗaga shi ya samu daman iya tashi, ƙatuwar yarinya kawai wanda bata san ta girma ba”.

Tashi zaune Aisha tayi amma bata bar jikina ba, tana hararan Hassan ta dube ni fuska a kwaɓe tace, “Yayah Hussain ɗina laifine idan na kwanta a jikin ka? Kaifa yayah nane ko”?, ta faɗa kaman zatayi kuka, riƙo hannun ta nayi na ɗan haɗiye yawon da ban san dalilin shiba, “Aisha yanzu ke kin girma, kuma islamically bai kamata ache kina hawa jikin mu ba yanzu, kinga gaskiya yayah Hassan ɗinki yake gaya miki, ki gyara kinji my dear”! na faɗa mata da yanayi na rarrashi.

Amma yarinyar nan ƙara shige mun jiki tayi tana mutsu-mutsu a jikina, dole Hassan ya taso ya figota ya kwaɗa mata mari, kuka iya ƙarfinta ta ƙwala, sannan ta fita da gudu tayi hanyar waje.

Cikin ƙarfin hali na dube shi nace, “me yasa ka mareta Hassan”? Tsaki yaja ya koma inda yake zaune yana operating laptop ɗinshi, sai jera tsaki yakeyi, daga baya ya ɗago ya dubeni, “My heart kasan wani abu? Wallahi idan naga Aisha a jikin wani namiji hankalina tashi yakeyi, ni na rasa me nakeji akan ta, bana son naga tana tarayyah da kowani namiji, gashi kullum na kwanta mafarkinta nakeyi, kai infact ma dai bari na gaya maka gaskiya, nifa ji nake kaman ina sonta, shiyasa bana son ta dinga zuwa inda nake, saboda ƙanwata ce, ban taɓa ganin irin wannan masifan ba”, ya faɗa kaman zaiyi kuka.

A razane na kalle shi, har wani rawa jikina ya keyi, “Hassan baka da hankaline? Kana tunani marar kyau Aisha ƙanwar muce wanda har abada babu aure a tsakanin mu, kuma koda a kwai aure a tsakanin mu kasan ni ya chanchanta na aureta ba kai ba”, na faɗa ina ture nawa laptop ɗin da yake ajiye akan table ɗin gaba na, bayan na gyara zamana ina kallon shi.

“Hussain amma kai jahili ne, Aisha ƙanwar muce, kuma na gaya maka koda aure tsakanin mu toh nine babbah ni yakamata na aure ta ba kai ba, garama ka daina wannan maganan, kuma kada na ƙara ganin Aisha a jikinka don sai na karya ta”, Hassan ya faɗa kaman wani zautacce.

“Lallai na yadda baku da hankali, ƙanwar taku uwa ɗaya uba ɗaya kuke muhawaran aurenta a tsakanin ku? Toh wani irin dabbanci ne kukeyi? Nawa ma kuke da har zaku fara maganan aure”? Ummi ta jeho mana tambayan bayan ta ƙaraso cikin parlourn.

Cike da kunya Hassan ya gaya mata yadda mukayi amma bawai da nufin muna son Aishan ba, saidai kawai don mu kwatanta hakan ne.

Ranta a matuƙar ɓace ta dube mu dukkanmu, wanda ni tun shigowarta na sunkuyar da idona a ƙasa, ina jinta tana cewa, “wallahi ko a mafarki na ƙara jin kunyi wannan tunanin toh da Babanku zan haɗaku, idan ba dabbanci ba meya haɗaku da son ƙanwarku uwa ɗaya uba ɗaya? Gaskiya kada na ƙara jin hakan ya faru daga yau a tsakanin ku, ko wanku idan ya tashi aure yaje chan wani wuri ya nemi matar aure amma ba Aisha na bakam, ku biyu mawa zan bayar idan ma da auren kenan a tsakanin ku, bayan duk ɗaya kuke a wurina, kada ku sake hakan”, ta faɗa tana duban mu dukkan mu.

Turo baki Hassan yayi yana duban Ummi yace, “toh Ummi kija mata kunne wallah ta daina faɗo mana ɗakin mu, kuma ta daina shigewa jikin mu, don ta girma, muma kuma mun girma, ɗon gaskiya dukkanmu aure mike so, gara ta daina chakuɗa jikinta dana mu”, ya faɗa yana dubana.

Bakin Ummi a buɗe tace, “Hassan yaushe aka yaye ka har kake cewa kana son aure? Tsabar baka da kunya nawa kake Hassan”?

“Ahh kaji Ummi dai? Wallahi aure muke so, ke Ummi kinsan irin namu halittan ne? Ni wallah ummi bazan wuce next year ba aure za amun, nifa kullum mafarki nakeyi da Aishan, shiyasa bana son ganinta a kusa dani, kuna ganin kaman bana sonta ne, wallahi Ummi kullum naganta sai naji dama bake kika haifeta ba, da babu abinda zai hanani aurenta”, Hassan ya faɗa yana duban Ummin, dama Hassan asalin shi mutum ne wanda baya jin kunya faɗawa su Ummi da Abba komai da ya shafe shi, don ina tuna ranan da yafara mafarki da mace sai da yagayawa Ummi muna zaune a ɗakinta, lokacin duka Ummi ta kai mishi, Abba kuma yace ta daina dukan shi, tunda ya zaɓi gayawa iyayen shi damuwan shi, kawai tana bashi shawaran da yakamata, haka muka tashi muka fita nidai cike da kunyan su Abba ranan.

Jin abinda Hassan ya faɗa ya saka Ummi zare ido tana duban shi ta kasa rufe bakinta, ganin haka na dube ta nace, “wallahi ummi nima haka nakeji, don Allah kice ta daina faɗamun jikina, ni narasa ma yanzun me yakawota har tazo ta faɗa mun jikina”.

“insha Allahu ta daina shigo muku ɗakin ku, yanzu ma tazo muku albishir ɗin zuwan Aunty Hauwa ce, amma kuka kama kuka daka mun auta na, kuma nasan Hassan ne mugun cikin”, ta faɗa tana kai mishi ranƙwashi.

Gocewa yayi yana dariya, “Ummi toh idan ba wulaƙanci ba, me yasa Aisha bata damu dani ba sai Hussain, tana shigowa fa faɗawa jikin shi tayi, me yasa ni ɗin bata faɗo jikina ba? Shiyasa na doketa saboda ta kiyaye gaba, don bana son ganin ta a jikin ƙattin maza”, ya faɗa yana shigewa ɗakin shi da gudu ganin Ummi zata sake kai mishi ranƙwashi.

Ajiyan zuciya nayi na mayar da kaina ƙasa ina wasa da wayan hannu na, kusa dani Ummi ta dawo ta zauna, murya a hankali tace, “Babanah! Aisha nina haifeta, bai kamata kubar sheɗan yayi galaba akan ku ba, ku daure ku ya fucheta a zuciyarku, dama akwai wani yayan matar Baba Umar da yace yana son Aishan har yayi magana wa Baban Narabi, amma ganin da mukayi Aisha yariyace, don yana da mata har da yara kusan uku, shiyasa bamu bada haɗin kai ba, don itama Aishan ta nuna bata so, amma idan munga zaku kawo mana tashin hankali wallahi zamu mishi magana ya fito, don ma yanzu baya ƙasan ne, idan ban da ku Aishan rabata za a yi wa ku biyun, ko kuma yayah kuke so ayi”? ta faɗa tana bina da kallo cikin tashin hankali daya bayyana a fuskarta lokaci ɗaya.

Hannunta na riƙo cikin nawa murya a hankali nace, “Ummi kiyi haƙuri kada abar Aisha ta auri wanda bata so, ni dai kawai bansan meyasa nake jin ta araina ba, amma Ummi baki tunanin ko an chanja miki ne a wurin haihuwarta? Don wallahi Ummi nifa son aure nake mata, nayi na daure naso wata yarinya da ta nuna mun tana sona amma firr Aisha ta hana zuciyata son kowa sai ita”.

A razane Ummi take kallona, “Hussain ɗina, Aisha nina haifeta, bakaga irin kamannin da ta keyi dani ba? Babu ɗayan ku da yake kama ni bayan Aisha, wannan ma ae ya isheku ishara”.

“hakane Ummi kiyi haƙuri, duk sharrin shaiɗan ne, kuma zamu kiyaye kinji, yaushe Aunty Hauwan zasu iso”?

Ummi tana murmushi tace, “sun wuce Narabi ne, suna fitowa nan zasu taho, kuma kutashi ku shiryah saboda taji daɗin ganin kun girma, ga Fatima idan ta girma ba sai a haɗaku da ita bama”?

Murmushi nayi ina kallon Ummi nace, “Ummi ƴar Fatiman nan wa zai iya jiranta? Maganan gaskiya ae Hassan ya miki ɗazu, mu bazamu wani wuce next year ba zamuyi aure, kawai ki fara shiri ke dai”, na faɗa ina dariyan jin kunya.

Dariya Ummi tayi sannan ta tashi tafita a ɗakin.

Ana idar da sallaɓ la’asar su Aunty Hauwa suka iso, a lokacin Ameer bai wuce 11yrs ba, Fatima kuma bazata wuce 9yrs ba, yaran sunyi wani irin girma da kyau sosai, duk inda sukayi kallon su nakeyi, don wani irin kama da Fatima da Aisha da sukeyi har ya ɓaci, Uncle Abdallah kamo hannun Aisha yayi ya zaunar da ita gefe yana duban ta cike da so kaman shi ya haifeta, yana dubanta yace.

“Baby na haka kika girma? Yaushe zakizo mana hutu? Tunda naji Baban Narabi yace wai har mun fara samun surakune, kina son Muhammad ɗin?”

Shagwaɓewa tayi ta kwanta a kafaɗan shi tana jijjiga kanta alaman ita bata son shi, ta buɗe baki tace, “Uncle nifa ya mun tsufah, ni nafi son miji irin Yayah Hussain, ni komai irin nashi nake so, don………” sai kuma tayi shiru ta rufe bakinta alaman ta tuna da wani abu, sai kuma tayi sauri ta kalli Ummi da ta zuba mata harara.

Dariya Uncle Abddallah yayi yana buga kafaɗanta yace, “kada ki damu baby nah, bazamu taɓa miki auren dole ba, asali ma wanda kike so zamu baki kinji baby nah”.

Dariya tayi tana kallon uncle Abdallah tace, “koda yayah Hussain ne uncle”?

“koda kuwa Yayah Hassan ne”, ya faɗa yana mata murmushi.

“Abdallah kutashi kuje kuhuta, bana son ka biyewa shirmen Aisha, taya zakana biye mata tana danganta kanta da ɗan’uwanta a aure kuma? Kasan yaran yanzu ba hankali ne da su ba”.

Dariya uncle Abdallah yayi bayan ya miƙe tsaye yana duban Abba yace, “Yayah kanajina da Ummi baka ce komai ba”? Abba yana kallon shi fuska a murtuƙe yace, “me zance maka naji kuna zuba shiririta kaida auta”.

Dariya uncle Abdallah yayi ya dubie ni yace, “Hussain idan ka amince ni zan baka auren Aisha don naga babu mai burge ƴata a duniya irinka, tun tana yarinya na lura da hakan, inaga kai ɗin kaine zaɓinta”.

“Uncle ae idan aure ne toh nine yakamata na auri Aisha, don nine babba kuma ni nake sonta ba Hussain ba, shi bai taɓa cewa kowacce mace yana so ba har yau, ni kuma ina sonta”, Hassan ya faɗa yana duban Aisha da take hararan shi.

Kallonta Uncle Abdallah yayi yace “wai doughter haka ne”? Turo baki tayi gaba tana hararan Hassan tace, “nikan bana son shi yayah Hussain ne yake burgeni, kuma nagayawa Ummi ni kan idan za’a mun aure yayah Hussain nake so, amma tace babu aure a e tsakanin yaya da ƙanwa”, ta faɗa tana kallon Ummin kaman zatayi kuka.

Tsawa Ummi ta daka mana da iya ƙarfinta, “ku wace kowa ya tafi ɗakin shi,” sannan ta maida kallonta kan Uncle Abdallah, “Bana son haka Abdallah, baka taɓa ganin irin kalan nawa ɓacin ran bako? Haka kawai zaka zo ka ɗaga mun hankali acikin iyalina, kasan ƴan biyu ne su, wa zan bawa………” sai kuma tayi shiru tana dafa kanta, Abba da sauri ya riƙo hannunta, “kanne Ummin su”?

Ɗaga kai tayi alaman hakan ne, sai lokacin Aunty hauwa da bata furta ko A ba tun lokacin da aka fara maganan sai yanzu, “Ummi BPn ki har yanzu yana yawan hawan ne”?

Ɗaga kai tayi alaman haka ne yana yawan tashi.

Cikin tausayawa Aunty hauwa take mata sannu da jiki, sannan uncle Abdallah ya dubi Ummi da murmushi yace, “Adda Allah ya baki lafiya, daga baya sai mu gama maganan mu, don wallahi burin Baba Umar kenan, kawai bai gaya muku bane, amma ni nan yagaya mun, shiyasa banga dalilin da zai sa a hana yara su fahimci su ɗin yayah suke a juna su ba”?

Ummi ta ɗago ta bishi da wani irin kallon tace, “haba Abdallah kasan yadda nake son Aisha kuwa? Ni so kake na zama bani da ɗiya ta mace? Bayan ko ita Hauwa ta manta da cewa Aisha ƴarta ce, ta haƙura mun da ita duniya da lahira sai kai yanzu zaka taso da abinda bazai taɓa kasancewa ba, idan nace zan aura mata Hissain toh Hassan kuma fah? Baka tunanin rabewan zumumcin yara nane? Gaskiya kubar maganan nan daga yau kuma anan wurin”.

“Haba Adda ni baki son haɗa zuri’an ki danawa ne kam? Wallahi Ummi babu abinda nake matuƙar buri irin ace Hussain ya zama miji wa Aisha, amma ke narasa me yasa baki da wannan ra’ayin? Ko dai nice baki son haɗa iri dani”? Aunty hauwa ta ƙarasa faɗa idonta cike da ƙwallah.

Runtse ido Ummi tayi ta cije bakinta, a hankali ta dubi Aunty hauwa, “Hauwa wallahi son da nakeyiwa Aisha ban taɓa jinshi kan Hassan da Hussain ba, asali ma tun ranan da na fara tozali da Aisha Allah ya saka mun sonta, toh ta yayah kike ganin ƴar da nake jin kaman ni na haifeta na barta ɗana ya aureta? Kalan watarana ya ƙuntata mata ni kuma bazan iya ɗaukan hakan ba? Kuma idan na amince yayah kike tunanin Aisha zataji na tsawon lokacin da ban barta ta san kece mahaifiyarta ba? Kuma yayah zanyi da Hassan da Hussain? Wallahi dukkansu sonta sukeyi”., ummi ta karasa faɗi tana share hawayenta.

“Wallahi kamuwan ubangiji ne Adda, bai kamata ki nemi haramta abinda Allah ya hallata shi tsakanin bayin shi ba, ke yakamata ki danni ɗaya daga cikin su, sai abawa ɗaya, kuma wanda yafi chan-chanta Hussain ne, wanda tun son da ya nuna mata tana jaririya Mahaifinta ya gaya mun Aisha matar Hussain ne, idan sun girma zai haɗa wannan auren a tsakanin su”, cewar Uncle Abdallah.

Kaman an jeho mu nida Hassan da tun fitan mu muke laɓe muna jin me suke cewa, Hassan da iya ƙarfin shi yace, “Wallahi ni zan auri Aisha, don kawai duk kunfi son Hussain sai kuce shi zaku bawa? Bayan shi ɗin bai taɓa cewa yana sonta ba, kunsan ton yaushe nake sonta”? Ya faɗa kaman zai sha kwalan uncle Abdallah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here