Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 43

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 43

5
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
@wattpad Aunty Nice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI and NUHU ARABI

SHAFI NA 43📑

__________📖 Gaskiya wannan hutun ya mana daɗi ba kaɗan ba, domin uncle Baba ma saida yayi three days tukun ya koma bauchi, ya gayawa Aunty hauwa ranan da zamu dawo zaizo da motan kasuwa sai ya ɗauke mu a motanta ya maida mu.

Munsha ziyaran da muka daɗe bamuyi ba, saboda Aunty hauwa badai zumunci ba kam, dama ita da uncle Baba babu inda basu shiga a dangi, Ummi ma tanayi amma bai kai nasu ba, uncle Auwal kam dama shi na ɗaki nane, don komai akeyi baka ganin shi a waje.

Kwanaki yanata tafiya, haka muka gama hutun mu Uncle Baba yazo ya ɗauke mu, tunda muka shiga mota Hassan ya fara mitan Aisha tana mishi rashin kunya, haka sukayi ta faɗa, Aunty hauwa na taya shi, muna isowa Darazo incle Baba yace Hassan ya dawo gaba ni na koma baya, don shi Uncle Baba baya son yaji an taɓa Aisha, don tasu ta zo ɗaya dashi, hakan Hassan ya fita yana hararanta ya koma gaba, ni kuma na dawo baya.

A bauchi Ummi ta mana shirye-shiryen dawuwa, ta tarye mu da girki masu daɗi, muna shiga nida Hassan da gudu mukaje mukayi hugging ɗin Ummi muna murna kaman mun shekara bamu tare, itama daɗin ganin mu ta keji sai shafa kanmu ta keyi, chan idonta ya sauƙa kan Aisha da ta zunɓura baki gefe tana hararan mu.

Da sauri Ummi ta ture mu a jikinta ta kamo Aisha tana faɗin, “waya ɓatawa autana ranta?” turo baki Aisha ta sakeyi tana hararan Hassan da shima hararanta yakeyi, ummi ta harare shi tace, “biyu ranka zaiyi mugun ɓaci akan autana fa, kai babu hali ku zauna inuwa ɗaya da ita sai ka ɓata mata rai? toh ka kiyaye ni”, ta ƙarasa faɗi tana janyo Aisha jikinta, nidai sai binsu da murmushi nakeyi, na ƙarasa gaban Aunty hauwa da take ta hararan Aisha da Ummi, karɓan Fatima nayi muka ƙarasa parlour muka zauna, Ameer kuma yana kwance akan kujera inda Uncle Baba ya kwantar da shi tunda muka shigo, wasa nakeyiwa Fatima amma idona yana kan Ummi da Aisha, don ganin wani irin sakalcin da Aisha ta keyi, dariya suke bani saboda ko kaɗan Hassan baya iya jurewa ganin hakan, amma ni ko ɗaya bai dame ni ba, saboda nasan daga Abba har Ummi da ƴan gidansu, Allah kaɗai yasan irin son da suke mun, don duk abinda ya shafeni kowa daban ya ke ɗauka, yanzu a zahiri Aunty hauwa sunfi jitawa da Hassan, saboda hayaniyar su tazo ɗaya, amma da zan nuna ina son wani abu, toh jiki na rawa Aunty hauwa take tashi tayi, ko chanji suka gani a face ɗina sai ya ɗaga musu hankali, haka su Uncle Baba da uncle Auwal ma, saboda haka ni duk wani kulawa da Ummi ke nunawa Aisha dariya nakeyi.

Ranan da Aunty hauwa ta gama hutunta zata tafi har kuka saida nayi, ba don komai ba sai don yadda nake jin baby fati a raina, kullum zan ɗauke ta nayita kallon ta ina kallon ɗan idonta masu masifar kyau irin na Aishan mu, wataran zan tambayi ummi nace, “Ummi kin taɓa ganin baby mai kyaun baby fati kuwa? Ummi nakan rasa ita da Aishan mu waya fi kyau ne”? Murmushi Ummi ta keyi tace, “har akwai wani halittah na mace da zai kai Aisha na kyau kuwa Hussain”? Tunin zakaji Aunty hauwa ta maida martani, “amma Ummi bakida kara, akan idona zaki ce ƴarki tafi tawa ƴar kyau? Gaskiya da sakel, kubani ma ƴata kafin kyaun ta ya kufce ya koma kan taku ƴar”.

Tana faɗin haka Hasan zai fara tarawa Aisha ɓacin rai ita kuma tayita kuka har sai da ƙyar nake rarrashinta tayi shiru, mun fito raka Aunty hauwa wanda Uncle Abdallah ya turo drivern da zai ɗauke ta da motan ta, har ƙofan gida muka rakota ina rungume da baby fati a hannuna, ita kuma Aisha ta riƙo hannun Ameer, don dama shi na hannun damanta ne, shi kuma Hassan yana rungume da Aunty hauwa kaman yaro ƙarami, muna tsaye a jikin motan na kasa miƙa mata baby Fatima, gaba ɗaya nayi kaman zanyi kuka, sai Ummi ta matso kusa dani don ta lura Aunty hauwa bazata taɓa cemun na miƙo mata fatima ba, muryan rarrashi Ummi take mun magana dashi.

“Hussain bata fatima mana kada suyi rana a hanya sosai, idan yaso sai muja mata kunne ta kula maka da Fatima kada ko ƙuda ya taɓa maka ita, don inaga hala ƴar gida za’ayi kaida babyn ka”, dariya suka fara mun ni kuma na miƙa fatima ina cewa Ummi, “haba Ummi lokacin da zan tashi aure ae ta mun ƙarama, 13yrs fa na bata, sai dai idan”…….sai kuma nayi shiru ina kallon Aisha da take ta wasa da hannun Ameer, sannan na dubi Ummi nace, “da Aisha ba uwa ɗaya aka haife mu ba da sai ita na aureta, don ina son baby fati ne don tana kama da Aishan mu, amma nafi son Aishan mu”.

Kallon Ummi Aunty hauwa ta tsaya tanayi, wanda itama Ummin duk sai ta ɗan razana da magana nah, “Hussain ae babu aure tsakaninka da Aisha, tunda nono ɗaya kuka sha, kaga ta zama ƙanwarka ko”.

Murmushi nayi ina kallon Aunty hauwa, “Aunty hauwa amma kema kinsan Aisha tafi kyau ko? Kawai bana son ranki ya ɓaci ne shi yasa nafi son Fatima, amma Aisha kullum tunaninta nakeyi, sai na tuna ƙanwata ce”.

Hassan yana hararan Aisha yace, “wallahi fatima tafi kyau, wannan ka dubi kanta fah ƙato ne, dama chanje akayi ita aka bawa Aunty hauwa, aka bamu baby Fatima, amma idan baka son baby fatima nikan Aunty hauwa ina sonta, idan ta girma zan aure ta ko”? ya faɗa yana shafa gashin baby fati.

“Insha Allahu kowa wanda yake so za’a bashi ya aura”, inji Aunty hauwa data faɗa tana hararan Ummi da wasa tana murguɗa baki.

Hararanta Ummi tayi sannan ta jawo hannu na tace, “rabu da Aunty hauwa, tunda Hassan yace yana son baby Fati zamu mishi kamu, kai kuma Allah zai baka taka wacce tafi Aishan mu kyau sosai, amma Aisha ƙanwar kace, kai zaka aurar da ita ma a wanda kaso idan ta girma”, ummi ta faɗa tana jan mu baya domin su Aunty hauwa su tafi.

Ta window Aunty hauwa ta turo kanta tana dariya tace, “Ummi duk abinda Allah fa ya hukunta wallahi bawa bai isa chanjawa ba, saboda haka kibar abinda yafi sanin ɗan’adam, kibar komai a hannun ubangiji, nidai ina tare da ra’ayin ƴaƴana har abada, jinina kuma mahaɗin jinin Adda na dana fi so sama da uwar data kawo ni duniya ne, saduwar alkhair Adda na”, ta faɗa tana ɗaga mana hannu dukan mu.

Tunda muka koma parlour Ummi ta zauna tayi shiru, ganin haka yasaka na tafi jikinta na kwanta nayi shiru, gefe ɗaya kuma Hassan ne suke ta faɗan su shida Aisha akan wallahi ta daina ruɗin kanta Fatima tafita kyau nesa ba kusa ba, ita kuma tana ta mishi tsigalan ae shiɗin tafi shi kyau, ya taso zai mareta nayi sauri na tare shi da hannuna, hararana yayi ya koma ya zauna, don Hassan duk iskanci idan na kalle shi yana bari, wanda kowa yana mamakin hakan da mukeyi a tsakanin mu, haka nima duk abinda nakeyi idan yace nabari toh nabar abin kenan har abada, haka duk abinda nake so idan ya nuna yana so toh na bar mishi, haka shima komai nake so ya bar mun kenan, sai dai hali kawai da yazo daban daban, amma muna son junan mu ba kaɗan ba.

Rayuwa babu wuya a wurin ubangiji, har yau muke shirin rubuta SSCE, wanda lokacin muke daf da cika 16yrs nida Hassan, inda Aishan mu kuma zata cika 11yrs, a lokacin kuma tana jss 1 a FGGC Bauchi, haka muka dage da karatu nida Hassan.

Aunty hauwa kuma bai daɗe ba suka bar ƙasan inda Uncle Abdallah ya samu lecturing a saudi, a wani university mai girman tarihi, bai samu matsalan tafiya da iyalan shi ba, tunda babu wuya suka bawa Aunty hauwa aiki a cikin school ɗin, so Aunty Fadila bata wani tayar da hankali ba, sun tafi da kusaɓ six month yazo ya ɗauke ta, daga lokacin kaman an tsayar da haihuwa a gidan su, don ko sau ɗaya basu sake haihiwa ba, amma Uncle Abdallah bai wani tada hankaliba, shidai ya gode Allah kullum yake cewa da samun Fatima, Allah ya raya mishi su kullum addu’an shi.

Kuma har zuwa lokacin mun ɗauka da gaske Aisha iyayen mu ɗaya da ita, don har Narabi muke zuwa hutu a matsayin gidan iyayen mijin Aunty hauwa, kuma Baban aminin Abban mu, kuma Abba ya saka mu tun muna yara kullum mukayi sallah mu dinga yiwa aminin shi kuma Baban mu, Baba Umar addu’a, kuma duk iya son gulmar ka bazaka taɓa gane Abba ko Ummi sun nuna banbanci tsakanin mu da Aisha ba, don yadda Abba yake nuna mata so to ko mu baya mana irin shi, don duk abinda Aisha tace a gidan shi akeyi, shi yasa kullum suna cikin faɗa ita da Hassan.

Abba london ya kaimu domin yin degree ɗinmu, ni Accounting na karanta, inda Hassan ɗina kuma yace shi Barrister yake so ya zama, saboda dukkanmu art class muke a secondry school, hakan yasa kowan mu ya zaɓi course ɗin da yafi sha’awa, ni nayi accounting ne saboda tun asali ina son yanda nake ga Abba yana shigan shi na zuwa office, kuma a tsari na nafi son naganni ima aiki a banki, amma Allah bai nufa ba sai na zama malamin makaranta, duk da farko bashi bani a raina, shi kuma dama Hassan Burinshi kenan ya ganshi a tsaye yana shari’a a gaban Alƙali yana baza hamata yana nuna isa,Lol Allah sarki ɗan’uwana, Hussain ya faɗa bayan ya share wasu hawaye da suka zubo mishi, sannan ya ɗago kanshi yana dubana yace, “Hummy dukkan yanayi da kamannin Aisha haka kike, shiyasa tun ranan dana fara ganinki naji tsoron ko Aisha ce ta biyoni, amma daga baya sai nayi tunanin babu yadda za’ayi Aisha ta zauna har yanzu bata girma ba, idan kuma ke Fatimace toh babu yadda za’ayi ya zama kina ƴar shekara 16, domin nasan yanxu duk inda Aisha take tayi 35yrs, Fatima kuma ta kai 27yrs, toh nayi tunanin ke ɗin ƴar Uncle Baba ce ko kuma uncle Auwal, saboda kamaninki da iyayena yayi yawan gaske, duk duniya akwai masu kama iri ɗaya, toh yanayi na ɗabi’un ku fah”? Sai ya juya ya dubi Daddy daya ƙura mishi ido.

“Humairah naso idan naga Daddy naga ɗaya daga cikin uncles ɗinane amma sai naga saɓanin hakan, amma duk da haka naji a raina keɗin ƴar’uwatace ko ta ƙauyen su Ummi ko kuma dai cikin garin misau, amma jikina yana bani ke ɗin ƴar’uwata ce ta jini”, sunkuyar da kanshi yayi ƙasa yana ajiyan zuciya mai ƙarfi.

Ni kuma da sauri na dubi Daddy nace, “Daddy wai hakane? Daddy Dr ɗan’uwa nane”? A ruɗe na jefawa Daddy tambayoyin lokaci ɗaya, shi kuma murmushi yayi yace, “sweet heart sauri da gaggawan na meye kikeyi haka? Mujira muji ƙarshen labarin Dr Hussain, sai suma suji ke ɗin daga ina kike? Kuma ki ɗin ƴar waye”?

A razane na tashi na tsaya nace, “nifa Daddy bana son kowa yazama Baba nah sai kai, nifa kaine kaɗai Daddy na”, na faɗa una ƙarasawa jikin shi na kwanta ina kuka.

Dariya Daddy yayi yana buga baya na yace, “Humairah na waya isa yace ke ba ƴata bace? ae sai na gille misho kai, ni na taɓa ganin inda uba da ƴa suke son junan su ma irin ni dake? Wallahi babu Humairah, keɗin ƴatace ta cikina, wanda nake jin son ta fiye da komai na rayuwar duniyan nan, saboda haka ki kwantar da hankalinki kinji sweet heart”!.

Gaba ɗaya parlourn yayi shiru sai sautin muryan kuka na da yake tashi a hankali, shiru kamar bazai cigaba da magana ba chan kuma sai yayi gyaran murya ya cigaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here