Zulum ya fitar da miliyan 62 domin tallafin karatu ga ɗaliban Shari'a da faransanci

Zulum ya fitar da miliyan 62 domin tallafin karatu ga ɗaliban Shari'a da faransanci

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya amince da fitar da Naira miliyan 62 a matsayin tallafin karatu ga dalibai marasa galihu da ke Borno a makarantun koyon fannin Shari'a da kuma wadanda ke karatun koyon harshen Faransanci.

Sakataren zartaswa na hukumar ba da tallafin karatu ta jiha, Bala Isa ne ya bayyana haka a yau Talata a Maiduguri.

Isa ya ce kudin ya kuma haɗa da siyan mota da gina sakatariyar kungiyar dalibai ta kasa, reshen jihar Borno, NUBOSS.

Ya yi bayanin cewa wadanda suka ci gajiyar tallafin karatun lauyan su ne dalibai 19 daga cibiyoyin koyar da aikin lauyanci shida da ke Najeriya, yayin da wadanda suka ci gajiyar harshen Faransanci dalibai biyar ne a jamhuriyar Benin da sauran daliban kasashen waje.

“Yaren Faransanci na da matukar muhimmanci ga al’ummarmu, kasancewar Borno tana iyaka da kasashen Kamaru da Nijar da Chadi da ke magana da Faransanci guda uku; shi ya sa Borno ke daukar nauyin mutane zuwa digiri na biyu a harshen Faransanci.

"Akwai shirin daukar nauyin mutanen da ke da sha'awar nazarin harshen Faransanci," in ji Isa.

A nasa martanin shugaban NUBOSS na kasa, Abubakar Wajiro, ya yaba da tallafin da gwamnatin Borno ke baiwa dalibai, ya kuma bukaci a yi ƙoƙarin ɗorewar tsarin.