Home Labarai Zargin daukar nauyin ta’addanci: Kotu ta mayar da shari’ar kwamishina a jihar...

Zargin daukar nauyin ta’addanci: Kotu ta mayar da shari’ar kwamishina a jihar Bauchi ga babban Alƙali

13
0

Zargin daukar nauyin ta’addanci: Kotu ta mayar da shari’ar kwamishina a jihar Bauchi ga babban Alƙali

Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ta mayar da shari’ar Kwamishinan Kuɗi na Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, ga Babban Alƙalin Kotu domin mika shari’ar ga wani alkalin na daban.

Alƙali Emeka Nwite ya ɗauki matakin ne a ranar Talata, yana mai cewa an fara sauraron shari’ar ne a lokacin hutun kotu, don haka ya dace babban Alƙali ya sake ba da ita ga wani alkalin.

Adamu na fuskantar tuhumar daukar nauyin ta’addanci da badakalar kuɗi tare da wasu ma’aikatan gwamnatin Jihar Bauchi guda uku, tuhumar da hukumar EFCC ta shigar a kansu.

An gurfanar da su a ranar 31 ga Disamba, 2025, inda suka musanta laifukan, kuma kotu ta ƙi ba su beli tare da umartar a tsare su a gidan yarin Kuje.

EFCC na zargin cewa tsakanin Janairu da Mayu 2024, waɗanda ake tuhuma sun bayar da kuɗaɗe har dala miliyan 2.3 domin tallafa wa Bello Bodejo da wasu da ake alaƙanta wa da ta’addanci, zargin da suka musanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here