Zanga Zangar Oktoba: 'Yan Sanda Sun Fadi Dalilin Gayyatar Shugaban Matasa 

Zanga Zangar Oktoba: 'Yan Sanda Sun Fadi Dalilin Gayyatar Shugaban Matasa 

Rundunar yan sanda ta gayyaci shugaban masu shirya zanga-zanga a ranar 1 ga watan Oktoban 2024. Rundunar ta gayyaci Juwon Sanyaolu wanda ke jagorantar kungiyar 'Take it Back Movement' da ta yi zanga-zanga a watan Agustan 2024. 
Kwamishinan yan sanda, Olanrewaju Ishola shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da The Guardian ta samu. 
Ishola ya ce sun gayyaci Sanyaolu ne da sauran mambobinsa domin tattaunawa kan lamura da dama da suka shafi Najeriya. Za a gudanar da ganawar a yau Laraba 25 ga watan Satumbar 2024 a ofishin kwamishinan da ke Ikeja a Lagos. 
Kakakin rundunar yan sanda a jihar Lagos, Benjamin Hundeyin ya bayyana yadda ganawar za ta kasance.