Zan Samarwa Bola Ahmed Tinubu Kashi 99.9% Bisa-dari na Kuri'un Yobe--Gwamna Buni

Zan Samarwa Bola Ahmed Tinubu Kashi 99.9% Bisa-dari na Kuri'un Yobe--Gwamna Buni

 

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

 

Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni a ranar Talata ya ce zai samarwa dan takarar Shugaban kasa a jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu kashi 99.9 bisa-dari na kuri’un jihar, a zaben shugaban kasa mai zuwa a watan Fabrairu.

 
Gwamna Bunii ya bayyana haka ne a lokacin da dubban ya'yan jam'iyyar APC a karkashin kwamitin kamfen din Tinubu/ Shetima (ICC) a wata ziyarar hadin gwiwa da suka kaiwa Gwamnan a gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu.
 
Ya ce jam’iyyar APC ta ci gaba da samu gagarumin goyon baya a jihar bisa la’akari da yadda gwamnatin sa ke kokarin samar da ababen more rayuwa da kuma ci gaban walwalar jama’a.
 
Gwamna Buni, wanda mataimakinsa, Alhaji Idi Gubana ya wakilta a gangamin gamayyar qungiyoyin su ka gudanar, inda ya bayyana jindadinsa dangane da yadda Kungiyoyin ke tafiya bisa tsari da neman hadin kan dukkanin kungiyoyin goyon bayan siyasa na jam’iyyar APC don tabbatar da an samu gagarumar nasara a zaben 2023. 
 
Gwamnan ya jaddada baiwa kungiyoyin cikakken goyon baya da kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu, inda ya yi kira ga ‘yan kungiyar da su kasance masu bin doka da oda a lokutan yakin neman zabe, a lokacin zabe da kuma bayan zabe.
 
“Ya kamata ku hada kai wuri guda ba tare da nuna wariya da jajircewa wajen tallata manufofin jam'iyyar APC a lokacin yakin neman zaben Tinubu/ Kashim; ku ci gaba da girmama kowa da kowa a lokacin da kuke gudanar da dukkan ayyukanku." In ji Gwamnan.
 
A nasa jawabin, mataimakin Ko'odinatan yakin neman zaben Shugaban Kasa na Arewa (ICC), Alhaji Umar Ibrahim, ya bayyana kwamitin a matsayin wata kafa wadda take hada kai da kungiyoyi daban-daban domin tabbatar da samun nasarar Tinubu/Kashim a zabe mai zuwa.
 
"Saboda haka wannan kwamitin zai jagoranci hanyoyin samun hadin kan al'ummar Nijeriya wajen bayar da ingantattun shawarwari don ci gaban kasarmu baki daya." Ya nanata.