Zan kawo karshen matsalar Garkuwa da mutane a Jihar Adamawa----Tinubu
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya yi alkawarin kawo karshen garkuwa da mutane da duk wani nau’in rashin tsaro a Najeriya idan har aka zabe shi a zaben da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu mai zuwa.
“Za a kawo karshen kashe-kashe da garkuwa da mutane,” Tinubu ya yi wa magoya bayan jam’iyyar APC alkawari a wani gangami da aka yi a Yola, babban birnin jihar Adamawa yau Litinin.
Tsohon gwamnan jihar Legas mai shekaru 70, ya kuma yi alkawarin samar da ayyukan yi ga matasa, samar da isasshen kiwon lafiya, ingantaccen ilimi da sauran “fa'idodin ci gaba” idan aka zabe shi.
Tinubu ya halarci taron ne tare da jiga-jigan jam’iyyar APC da suka hada da shugaban kasa Muhammadu Buhari da ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa a jam’iyyar, Aisha Ahmed wanda aka fi sani da Binani.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya ce jam’iyyar APC ba maza kadai take da su ba, tana da ‘yan mata masu iya aiki kamar yadda ya bukaci magoya bayan jam’iyyar da su kada kuri’a a Binani.
“Za mu yi muku aiki yadda ya kamata, za mu ba ku aiki yadda ya kamata,” Tinubu ya shaida wa magoya bayan jam’iyyar a wajen taron.
“Za mu kula da bukatunku, tare da Binani tare da Shugaban kasa, Bola Tinubu insha Allahu (In sha Allahu), za mu kawo muku ci gaba, ilimi, lafiya, walwala, za ku samu ruwa mai kyau. a sha, za a kawo karshen kisa da garkuwa da mutane."
managarciya