Zaman Lafiya Zai Dawo A Nijeriya----Atiku Abubakar

Zaman Lafiya Zai Dawo A Nijeriya----Atiku Abubakar

Atiku Abubakar dan takarar jam’iyar PDP na shugaban kasa a 2023 ya ce zabarsa ya wakilci jam’iya  tarihi ne aka kafa da zai sauya lamurran tafiyar da gwamnati da siyasa a Nijeriya.

A jawabinsa na godiya bayan ya lashe zabe Atiku ya tabbatar da kudirinsa na kawar da bata gari da suka hanawa kasar nan zaman lafiya da wadan da suka bata tattalin arzikin kasa.

Ya ce za su samar da aikin yi da cigaban kasa, za a gyara abubuwan tafiyar da gwamnati da jam’iyar APC ta bata a lokacin mulkinta.

Ya yi kira ga abokan takararsa da su zo a hada kai a gina jam’iya duk wanda aka batawa rai sai ya yi hankuri.