ZAMAN JIRA: Fita Ta Biyar

Kowace rana da kalar motar dake zuwa wajenta, manyan mutane su ne ke zarya  gun Nusaiba tun kafin ta ida amsa sunanta na budurwa.  Ganin haka yasa Alh. Ibrahim ce ma Nusaiba ta fitar da miji ya yi mata aure ya gaji da tara mai maza a ƙofar gida, shi gidanshi ba dandalin tara maza ba ne ba. Ai sai Kande ta zaburo kamar ta ji wani

ZAMAN JIRA: Fita Ta Biyar

ZAMAN JIRA


               *NA*
*HAUWA'U SALISU (HAUPHA)*



                        Page 5

"Malam kace min dole na daina sallar ranakun Alhamis da Juma'a da kuma Litinin. Sannan dole na daina alwala idan zan yi sallah a gidan Jabeer. Kace dole ne na dinga yin sadakar nono tsala duk ranar Lahadi amma na tabbatar da cewa nonon gun Bafulatana fara tas na saye shi, kuma kar da na yi tayi duk yadda tace kuɗin nonon in ɗauka in bata. Sannan babu ragi balle ragowa a tsakanina da Jabeer, sai kuma na ƙarshen shi ne kar da na sake taka ƙafafuna gidanmu da gidansu Jabeer har na tsawon shekaru goma cif. To zan yi duk yadda nake so haka tauraruwata zata haskaka ko'ina a duk inda nasa ƙafafuna ba wadda za a gani sai ni. Kuma kuɗi ba matsala bane a guna sannan duk namijin da ya zo guna shike nan ba zai taɓa iya barina ba kuma sai yadda na yi da shi."
Malam Habu ya dinga ɗaga kai kamar ƙadangare har ta kai ƙarshen zancenta. Sai kuma ya haɗe rai ya ce,  "Gayamin wanne ne ki kai kuskure daga cikinsu ko kika daina aikatawa?"  Ƙwal-ƙwal hawaye suka zubo mata daga ido tace,  "Duk ina aikatawa Jabeer ɗin ne yanzu ya daina shiga lamarina kwata-kwata balle na yi mai rashin mutuncin...'"Ƙarya ki ke matsiyaciya, don haka ki je gida cikin jikinki shi ne hukuncinki, gobe ma ki sake aikata abin da kika aikata za ki gani a ƙwaryar idonki ja'ira. Maza ki aje na sadaka ki wuce ki ban waje."  Jikinta na rawa haka ta aje bandir ɗin 'yan dubu guda biyu ta fice jikinta nata rawa. 
Tana shiga gida kanta ya cigaba da sarawa, tana son cikinta tana son rayuwar da take, ya kenan za ta yi? Malam Habu tun da ya ce zai ɗauke cikin tabbas sai ya ɗauka, amma ita kam ba za ta so hakan ba. To amma kuma idan bata so hakan ba so take tauraruwarta ta shige duhu ne komai ya cakuɗe mata ne? Tabbas tana rayuwa a zahirance za a iya kiranta da rayuwar jin daɗi, amma ƙarya ne, rayuwarta cike take da tashin hankali da firgicin gaske. Wace irin rayuwa ce wannan wadda na waje na ganin abar birgewa ce amma kai dake cikin ta kasan abar tsoro ce? Nan da nan ta fara zagayen ɗakin tana tuna shekarun baya na farkon aurenta da Jabeer.

         SHEKARUN BAYA

Tun da Nusaiba ta taso ake ɗauki ba daɗi tsakanin iyayenta saboda mahaifinta mutum ne mai gudun duniya da tsentseni, amma Mama Kande duniyar ta kawai take ci da tsinke. Tabbas zaman Mama Kande da Alh. Ibrahim zama ne na haƙuri da kau da kai a cikin gidan domin dai wuta da ruwa ne aka haɗa wuri guda. Saboda Alh. Ibrahim bai sa duniya a  gaba ba, kamar yadda matarsa Kande ta ɗauki duniya wata tsiya ba. Da ka ji bakinsa a cikin gidan to wa'azi ne yake yi wa Kande kan ta rage son abin duniya amma tamkar taki yake ƙarawa shuka. Kande ta sha duban shi tace, ita wallahi ta rasa ya akai ma ta aure shi, shi ba wata dukiyar a zo a gani ba don sai dai ace rufin asiri mutumin da bai iya baka kyautar miliyan ina kuɗi suke a gun shi. Ita sauƙin ta ɗaya da shi kyan da gare shi, to duk yadda ranta ya ɓaci sosai takan ji sanyi idan ta tuna da cewa za ta fanshe a gun yaran da za ta haifa duk wasu kuɗaɗe da bai bata ba to za ta amshe su a gun maneman yaranta don haka kodayaushe addu'a take Allah Ya bata yara mata da yawa kyawawan gaske waɗanda za su kawo mata dukiya har gida. Sai dai da yake an ce kana naka tsarin Allah na nashi nufin sai da Kande ta haifi yara biyar duk maza a jere sannan ta haifi ɗiya mace guda ɗaya, daga nan haihuwar ta tsaya cak. Tun Nusaiba na yarinya ake ɗauki ba daɗi tsakanin iyayen saboda kowa burinsa daban akan ta, shi dai uban babban burinsa shi ne ta fara sauke Alqur'ani kafin ya kaita makarantar boko, ita kuma Kande tace bai isa ba ai ba namiji ba ce balle a ce sai tayi karatun almajirai irin na yayyenta maza ba. Saboda haka duk lokacin da uban ya ce ta shirya ta tafi islamiyya sai uwar tace bata lafiya, ko kuma tace aikenta za tai idan ta dawo za ta je. Kande ta ɗauki son duniya ta ɗaura wa Nusaiba, idan an magana sai ta ce ita ce duniyarta a barta ta sakata ta wala kawai saboda ba wani ya haifar mata ita ba ai.  Cikin wannan halin na yau a je gobe a ƙi zuwa haka Nusaiba tai ta karatun duka ɓangarorin ba bokon ba haka ba arabin ba. Kodayaushe huɗubar da Kande ke ma Nusaiba ita ce, "Yarinya ki saki jiki ki kalli kowa da idanunki domin ki shaida wanda za ki taimakawa da wanda za ki sa a rufe gida idan ya zo gun ki, saboda na lura baƙin ciki ake maki akan abin da za ki zama nan gaba."  Nusaiba ta taso cike da gata marar iyaka wanda komi ta yi daidai ne kaf yayyenta maza ba wanda bata raina ba, kowane a cikinsu ba wanda take gani da gashi, idan suka nemi su hora ta sai Kande ta haukace masu ta kama zagi tana cewa duk wanda ya shiga tsakanin farin ciki da yarinyarta sai inda ƙarfinta ya ƙare.
Lokacin da maƙerin budurci ya fara ƙera Nusaiba samari suka fara yo mata caaaa, sai Kande ta rasa ina za ta saka kanta don murna da farin ciki, abin da ya kawo mugun saɓani tsakanin Nusaiba da mahaifinta da yayyenta maza kenan. Sai dai Kande ta zame mata katanga ga duk wani hayaƙi da zai taso daga mahaifinta ko yayyenta. Alh. Ibrahim yana jin ɗaci da takaicin halin da Nusaiba ke ciki sanadin Kande. 
Kowace rana da kalar motar dake zuwa wajenta, manyan mutane su ne ke zarya  gun Nusaiba tun kafin ta ida amsa sunanta na budurwa.  Ganin haka yasa Alh. Ibrahim ce ma Nusaiba ta fitar da miji ya yi mata aure ya gaji da tara mai maza a ƙofar gida, shi gidanshi ba dandalin tara maza ba ne ba. Ai sai Kande ta zaburo kamar ta ji wani mugun abu tace,  "Kan uban can kayyasa! Me nake ji kana cewa ne wai ? To bari ka ji na rantse da Allah baka isa ba, ai ba kai kaɗai kake da iko akan ta ba ni ce nan na haife ba kai ne kaɗai ka haife ta ba, don haka alhakin aurar da ita har da ni ya shafa ba kai kaɗai ba. Don haka ka bari idan naga lokacin da ya kamata tai auren ya yi da kaina zan fitar  mata da miji na aurar da ita ba sauri nake ba yanzu. To me ma na sama ya ci balle ya jeho ma na ƙasa ban da neman bala'i irin naka Alh.?"  Shi kuma  ya tsaya kai da fata kan maganarsa ta cewa Nusaiba ta fito da miji idan ba haka ba shi zai fitar mata da shi. Ganin da gaske yake yasa Kande ta haɗa ma Nusaiba ta kayanta tas ta tura ta gidan wata ƙawarta wadda halinsu ya zo ɗaya tace ta zauna sai Alh. Ya gama haukansa ta dawo gidan amma ba za ta tsaya tana ji tana gani ba kwaɗo ya yi mata ƙafa ba, kawai yarinyar ta fara kawo mata kuɗaɗe da manyan mutane shi ne don baƙin ciki zai ce wai tai aure, ai hakan ba zai taɓa faruwa ba ko bayan ranta, don haka za ta dage ta koya wa Nusaibar yadda za ta tatsi kuɗaɗe daga gun maza domin so  take gidan Nusaiba ya zama aljannar duniya wanda babu irin sa a duk cikin amaren da akai ma aure a shekarar da Nusaibar tai aure.  Shi ne don  tukungwiwar tsiya za a ce wai ta fito da miji ai mata  aure, a'a goro za ta zama ba aure za tai ba.  Ba zata taɓa bari tarihi ya maimaita kansa ba a kan 'yarta guda jal da Allah Ya bata domin ta share mata hawayenta ba. Ita kanta ba don yanzu zawarcin ba daɗi zai mata ba ai da ta ɓalle ta kama shi da kyau ta wanki Alhazan birni, to matsalar tsufa ya fara yi yi mata baƙin ciki, amma da ko da wa Alh. yake yawo sai ya sake ta ta cizgi rabonta itama a gun mazan, shi ne don neman a cusa mata baƙin ciki za a ɗauki yarinyar daga tasawarta ko me bata samar mata ba ta samar wa kanta ba za a ce wai ta fitar da mijin aure chab abin da ba zai yiwu ba kenan. 
Sai da Nusaiba ta yi wata sannan ta dawo lokacin idonta ya buɗe sosai yadda hatta uwar tata nuna mata take tafi ƙarfinta abin da ya sake taɓa zuciyar mahaifinta da danginta maza kenan, ita kau Kande sai ta ji daɗi ta kira ƙawarta tai ta mata godiya wai ta wayar mata da yarinya abin ya yi mata daɗi.   
Wasa-wasa sai da sunan Nusaiba ya ratsa ko'ina a garin kowane namiji bai cika ɗan iska ba idan ba a gan shi yana yawo da Nusaiba a cikin motarsa ba. Nusaiba ta sake cika ta tumbatsa sosai ta zama dakekiyar budurwa ga kyau ga kuɗi hakan yasa kodayaushe ita da uwar suna wajen malamai wai neman maganin baki da kuma kwarjini da sake haskaka a idanun maza.
Duk wannan artabun da ake ashe tuni Alh. Ibrahim ya yi wa Nusaiba mijin aure jira kawai yake yaron ya dawo daga karatunsa ɗan gidan abokinsa ne kuma amini watau Alh. Habeeb.  Duk lokacin da Baban Nusaiba ya je ma abokinsa da maganar halayen Nusaiba da uwarta sai abokinsa ya ce ya ƙara haƙuri in sha Allah komi zai zo ƙarshe nan da wani lokaci. Duk da cewar Alh. Habeeb na sane da munanan halayen Nusaiba amma yasa a ransa zai zama silar share ma abokinsa takaici akan ta, don haka ya kira ɗansa Jabeer dake karatu a India ya gaya mai ya yi mai matar aure kar da ya kuskura ya fara son wata yarinya a ko'ina ma take ko yake shi. maganar ta razana shi domin a kwai wata yarinya guda data nace mai a cikin zuciya tun da tana yarinya yake dakon sonta bai taɓa tsammanin zai samu matsala daga mahaifinsa akan ta ba sai dai ko mahaifiyarsa da sauran dangi saboda yana binciken yarinyar ya ga yadda ta koma marar ji idonta ya buɗe da yawa. Ya so ya fita sabgarta amma abin ya ci tura kodayaushe ƙara jinta yake a cikin ransa da zuciyarsa don haka ne duk lokaci zuwa lokaci yake bibiyar rayuwarta.
Har ciwo ya yi ya dinga jin tsanar yarinyar data zama katanga tsakaninsa da cikar burinsa don haka da ya gama degree ɗin sai ya tsiri yin masters ɗinsa a can don ma kar ya dawo ya ga ganta ko a ce a yi maganar auren. Babu yadda bai ba ya cire son yarinyar da yake rainon sonta a ransa ya kasa, don haka sai ya yanke shawarar kiran mutane ahaifinsa ranar da ya kammala karatunsa baki ɗaya domin ya fayyace mai gaskiyar magana akan yarinyar gidan abokin Baban da yake so mai suna Nusaiba. Sai da ya gama kora bayani tas sannan Alh. Habeeb ya yi murmushin jin daɗi ya ce,  "Kwantar da hankalinka, domin ita ce matar da nayi maka nake jiran ka dawo ka aure ta, amma fa ban san tsananta bincike ko ɗaukar jita-jita balle biye wa tsogumin mata, kai dai ka aure ta da , zuciya guda ka kuma ci-gaba da ƙaunarta kana yi mata addu'a in sha Allah za ta zama matar rufin asiri a gidanka." 
Sosai Jabeer ya yi farin ciki da jin cewa Nusaiba ce zaɓin mahaifinsa don haka sai ya yanke shawarar fara kiranta ko a waya ne suna gaisawa. Ranar da ya kira ta lafiya lau suka gaisa ya faɗa mata ya jima yana dakon sonta kuma da aure ya zo gare ta, amma sai ta ce aure ba yanzu amma soyayya salamu alaikum idan ya yarda. Duk da yasan fiye da haka  zata aika amma ya yi mamakin jin cewa ita ba aure a gabanta soyayya ce kawai tasa gaba a halin yanzu sai mamakinsa ya koma tashin hankali na gasken-gaske. Saboda shi babban burinsa ya auri Nusaiba ya killace ta a gidansa ya maida ta sarauniyar kaf mata duniya. A haka dai ya ci-gaba da biye mata har ya fara shirin tattarowa ya dawo gida duk da a can sun nemi su riƙe shi ya yi masu aiki ya ce a'a saboda yasan idan ya amsa ba lallai iyayensa su ji daɗi ba haka zalika ba mamaki aurensa da Nusaiba yana iya samun matsala don haka ya bar masu kayansu ya dawo gida Nigeria.
Bayan ya dawo ne tashin hankali ya ɓalle sosai a tsakanin gidajen biyu, domin shi dai Jabeer kaf gidansu mahaifinsa kaɗai ke son auren sauran babu mai ƙaunar auren saboda halayen Nusaiba da mahaifiyarta. To a can kuma gidansu Nusaibar fama mahaifin ke yi domin ita da uwar sun koma gefe guda sun ce ba za su taɓa yadda da wannan aure ba sam. Shi kuma uban ya ce basu isa ba akan auren har sakin Kande ya yi amma duk da haka jikinta bai sanyi ba, sai ma take jin gwara da ya sake ta yadda za ta ci karenta ba babbaka akan Nusaibar. Mutane da dama sun nuna mai ya yi kuskure don haka ya maida ta ɗakinta tana ta yi mai izgili da cewar aure fa ba yanzu bata ma yadda da aikin yaron ba ta ya zata ba shi auren yarinya? Ita fa a yadda ma tai bincike Nusaiba tafi yaron arziƙi to akan me zatai auren ci baya ta auri wanda tafi ƙarfi? Babu irin tashin hankalin da ba ai ba, amma dai iyayen maza suka kafe akan dole sai an yi wannan auren ba fashi. 
Jabeer babu irin cin fuska da wulaƙancin da Kande ba tai ma shi ba, haka ita ma uwar gayyar amma ko a jikinsa, sai dai ya bata haƙuri ya jaddada mata irin ƙaunar da yake ma Nusaiba ba ƙarama bace ba. Akwai lokacin da suka kira shi suka saka shi a tsakiya wai ya faɗi farashinsa za su biya shi ko nawa ne indai zai ce ya janye. Amma ya ba su haƙuri ya ce yana son matarsa a bar shi ya rayu da ita.
Sanin cewa gidansu Jabeer babu mai na'am da auren sai suka tsiri zuwa gidan su yi rashin mutunci, ranar farko Kande ta je ita da ƙawarta ta tabbatar masu da cewar ita 'yarta tafi ƙarfin auren yaron su don haka tun kafin dare ya yi masu su je a daidai su, su samar ma shi mata amma Nusaiba ko a direbanta bata iya ɗaukar Jabeer aiki. 
Da yake gidansu Jabeer ba kamar gidansu Nusaiba, sai kowa ya yi banza da su ya ƙyale saboda sun san duk wanda ya tanka ma su idan maigidan ya ji labari sai ransa ya yi mugun ɓaci, tsaye yake a gidansu Alh. Habeeb bai barin ɓaraka daga gidansa. Wannan kawai yasa su Kande suka gama cin mutuncinsu ba wanda ya ce masu ko ƙala kaf gidan sai dai sun ƙara dasa tsanar Nusaiba a zukatan mutanen gidan sosai.    Bayan sun fito ne Kande ta dubi ƙawarta Jummai tace,  "Kin ga 'yan jarfa, duk rashin mutuncin da muka tsiyayar masu ko a fuska ba wanda ya nuna mana ya ji ba daɗi balle su biye mana anya kuwa kina ganin ba abin da mutanen nan suka taka ƙawata?"    Jummai tai dariya tace,   "Ai maigidan ba ƙaramin ƙwallon ɗan iska bane, mugun tsoron shi suke don haka su ka ƙyale mu, bayan nasan hakan da abin da zai sa na raka ki gidan kai tsaye sai dai mu bi masu ta bayan gida kawai. Shin wai ma duk abin nan da ake kin taɓa kai sunayensu gun Bokan Tabki kuwa ƙawata?"   Kande ta ja ajiyar zuciya tace,  "Kin san halina dai da biye-biye, to duk inda kika san muna zuwa na je har ma inda baki sani ba na je amma abin ya ci tura, maimakon magana ta ɗauki lalacewa sai ƙara haɓaka take, takaicina shi ne yanzu yarinyar nan take gaɓar cin kuɗin maza, yanzu ne maza suke ƙwanƙwasa mata ƙofa amma don butulci da mugun jin zafi shi ne Ibrahim ke son aurar da ita ban ci komai ba, lamarin nan ya yi min tsaye har rama nake na rasa kwanciyar hankali na rasa natsuwa ga dukiya ina kallo ana mun jin zafi. Tabbas na yi nadamar auren Ibrahim ba adadi ƙawata zuciyata har ciwo take min kan lamarin nan...ta fashe da kukan baƙin ciki. Jummai ta ja ajiyar zuciya don har ga Allah bata taɓa ganin shegen da asiri bai kamawa kamar mijin ƙawarta ba Ibrahim, shekara da shekaru suna abu  guda kanshi amma ba wani sauyi daga gun shi dole suka haƙura suka saka mai ido tun can fil'azal yanzu kuma a kan Nusaiba babu irin asirin da ba su banka mai ba amma duk a banza wai an tsikari kakkaura. Ta sake duban ƙawarta Kande tace, "Me zai hana a je a sakawa yaron tsanar ta ne a huta, ai dai sai idan yana son ta ne za a ɗaura auren ko? Kande tai dariyar takaici tace, "Ashe baki da labarin yaron tsabar karatun Alkur'ani har ya haddace shi a kansa, Allah kaɗai yasan iyakar littattafan addinin dake cikin kansa. Ke duk abin ba sauƙi ta ko'ina so ake a raba ni da arziƙina kin ji."   Tashin farko ai ta kansa muka fara, na je gun Boka na Tudu na amso haɗi na musamman ya ce a zubawa shegen a cikin naman zabo haka na dage da kaina na shiga kichine na yi mai dahuwar daddawa don kar da kalar rubutun ya bayyana naman zabo ya dahu ya ji kayan haɗi don  rabon da na zage na yi irin wannan girkin tun ina budurwa sai fa a ranar, in kai ki ƙarshen zance yaron nan ya zo muka tasa shi gaba da daɗin baki don ya ci, da farko ya ƙi ci sai da muka dage sannan fa yaron nan  ya yi bisimililla ya shiga kwasar gara yana jifar mu da munafikin  murmushi muna ta murna an gama da matsalar ashe ba mu san ko a kan halshen shi asirin bai zauna ba. Sai ma ya sake dagewa yana ta turo mata saƙon bai taɓa cin nama mai daɗin wannan ba don Allah ta sake yi mai irinsa wata rana idan ya zo. Ke na takaita maki labari har magani aka ban na bi dare na je ƙofar gidansu yaron nan na yayyafa wani na binne wani na watsa wani amma duk a banza kamar an aiki loma gewayar wuya haka asiran da nake jibgawa suke wucewa ban ganin alamar komi, don haka ban san ya zan yi ba daga ni har ita yarinyar ba."
Jummai ta nisa tace, "Me zai hana ki tura ta gun danginki ki gaya masu baki son auren da ubanta zai mata ga ta nan su aje maki ita sai ya janye zancen auren ta dawo gunki?"    Kande tai murmushin takaici tace,  "Dangina duk 'yan son zuciya ne bayan Ibrahim suke, lokacin da na turo ta gunki har gida suka yo gayya suka yi min wankin babban bargo da tofin alatsine. Ke dai mu nemi wata mafitar kawai ban da wannan don su ma cike suke da hassada kamar yadda ubanta ke min suma sammakal ɗin ne.  Haka dai sukai ta neman mafita amma ba matsaya dole suka rabu ba tare da sun samu mafita ba. 
Ba su ankara ba sai ga iyayen kayan lefe an kawo abin da ya ja Nusaiba tada aljanun ƙarya kenan ta fice da gudu tana ihu kai ba ko hula mutanen unguwa suka kamo ta suka dawo da ita cikin gidan suka iske Kande nata kuka ta tasa kayan lefe ga masu kawo lefen zaune suna kallon ikon Allah. Kishiyar Mamar Jabeer ɗin ta dubi mutanen unguwar tace, "Don Allah ku gaya mata, mu ke da kuka ba ita ba, ita kukan daɗi take."  Nan dai jama'ar unguwa suka taru suka ba su baki sosai 'yan kawo lefe ko ruwa ba a basu sun sha ba suka juya.

Haka akai auren ba don ran Kande na so ba sai dan maigidan yafi ƙarfin su haka shi ma Jabeer gidan nasu kamar ba biki ake ba don ba mai son haɗin daga shi sai Babansa ke son auren.
Tsabar iskanci ko ƙawa ɗaya babu a tare da Nusaiba haka aka kaita gidanta mai kyau daidai misali, amma tun kafin jama'a su watse ta dinga zagayawa tana cewa bata iya rayuwa cikin gidan nan kamar wani akurki dole ya sauya mata gida idan ba haka ba sai dai ya sake ta, duk da dama ba zama ta zo yi a gidan ba, zaman jiran wa'adi take a gidan domin tasan duk daren daɗewa sai Jabeer ya sake ta tun da bata shirya zaman aure ba.
Sanin hali  yasa shi ma bai jawo ko aboki guda ba, shi kaɗai ya shigo gidan, domin ya sami labarin irin abubuwan da ta yi da aka kawo ta gidan a gaban danginsa.   Ba kowa gidan tace a tafi a bata waje tun da an kawo ta zaman uban me kuma za ai mata a cikin gida? Hakan yasa kowa ya watse yana jinjina rashin daraja irin tata. Ba danginta ba haka ba dangin angon ba.
Wanka tai ta fito falo ta zauna ta saka wasu shegun kaya sai ƙamshi take yi, don Nusaiba ba baya ba gun kwalliya. Wayarta ta ɗauka tana chat da samarinta tana gaya masu an yi mata auren dole amma kar da su damu har gobe ruwa na maganin dauɗa. Da dama sun mata fatan alheri da nasiha suka ce kuma ta goge number su suma za su goge tata, yayin da wasu kuma suka ji daɗin lamarin domin dai ba aure ya kawo su ba tun farko dama zuwa su kai su kwashi rabonsu sai ubanta da yake yana da wayau ya yi mata auren wuri kafin su shaida komi to ga dama ta samu don haka suka tabbatar mata da ba komi kuma duk abin da take so bata da matsala ta yi magana kawai. Tana cikin chat ɗin ya shigo ko kallon inda yake ba tai ba sai ma gyara zama tai wanda hakan yasa baki ɗaya hankalin Jabeer ya koma kanta. Gabansa ya faɗi ganin  wata hatsabibiyar riga dake jikinta baki ɗaya ko'ina na jikinta a bayyane yake ga ƙamshi na tashi a falon yasan kau na jikinki ta ne, madadin ya wuce ya aje kayan hannunsa sai kawai ya isa inda ta zauna yana yi mata sannu. Harara ta watsa mai ta ja uban tsaki ta aje wayar gefe guda ta mike tsaye ta yi ɗan taku ɗaya zuwa uku sannan ta tsaya tana kallonsa tace, "Jabeer ka yi wauta daka biye ma ubana ka aureni domin kuwa ni ba sa'ar aurenka ba ce ba, haka zalika ba zan taɓa dawwama a cikin wannan akurkin gidan ba, idan ma zaka tsaya a zaman jira ka tsaya idan kau ba haka ba zaka wahala zaka shiga cikin tashin hankali daidai gwargwadon yadda ka amince wa ruhinka. Sannan ina so ka sani babu ruwanka da ni da lamurrana balle shiga cikin hidindimuna kowa ya yi zaman kansa a cikin gidan nan na gaya maka ba zan iya aure yanzu ba sam ni, amma saboda naci da rashin zuciya shi ne ka nace ka jajirce sai da ka kawo ni gidanka. To ka sani madadin farin ciki baƙin ciki za ka samu daga guna, haka zalika burinka ka takurawa rayuwata ka cusa ma uwata takaici ka hana burinta cika to na tayaka murna ka ci wannan nasarar amma nasara ta gaba tawa ba ce ba taka ba Jabeer." 
Ajiyar zuciya ya yi duk da ya ji zafin maganganunta amma dai hakan ba zai sa ya biye mata ba a ranar farko su kafa tarihin aurensu da faɗa ba. Don haka ya dube ta fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce,  "Allah Ya baku haƙuri baki ɗaya amma dai ki sani a wajena baki da matsala zan zame maki duk yadda kike buƙata zan baki farin ciki haka zan musaya maki baƙin cikinki zuwa farin cikina, ban damu ba ko da ni zan kasance cikin baƙin ciki ba indai ke kina cikin farin ciki to ya wadatar."
Baki ta taɓe don ba haka taso ba, so ta yi ya biye mata su zubar da ruwan rashin mutuncin da zai fusata ya narka mata saki ko guda ne a cikin daren farkon nasu. Shi kam kamar yasan komai sai ya danne zuciyarsa dama bai taɓa ji a ransa zai biye mata ba ko ya zama yana biye ma duk abin da za tai ma shi ba, yana da tabbacin za a wayi gari ta gane gaskiya ta dawo ƙarƙashin imuwarsa kamar yadda kowacce mace take da mijinta. Don haka zai zaman jira ko da kuwa zaman zai kai shi a ranar ƙarshen rayuwarsa ne zai jira.  
Da kanshi ya ɗauko duk abin buƙata ya juye kazar da ya shigo da ita ta musamman da wani abokinsa ya ba shi ya tabbatar mai da cewa ya samu ko ya ne amarya ta lasa kazar nan sai ya gode mai sau ɗari cikin daren kafin gari ya waye. Baki ɗaya ya tura mata kazar ita kam don ta ba shi haushi sai kawai ta ci-gaba da cin kazar hannu baka hannu ƙwarya, tana gamawa ta ja tsaki wai bai  kawo mata ruwan wanke hannu ba.  Da sauri ya ɗebo mata ruwan da wajen da zata wanke hannun yana ta murmushi don so yake ya ga ƙarshen lamarin kamar yadda abokinsa mai kaza ya ce yana cikin alheri dumu-dumu.
Kamar wasa Nusaiba ta dinga jin kasala ba kasala ba wani tsamm jikinta ke yi don haka ta gyara kwanciyar ta akan doguwar kujerar da take kawai tana jinta kamar ta banki kayan aiki bayan tasan sau ɗaya ta taɓa kora su bata sake ba don ta sha wuya. 
Jabeer ya ci wadda ta rage ya kwashe komai ya gyara gun ya shiga ya watsa ruwa ya yi sallar godiya ga Allah sannan ya saka 'yar jallabiya gajera ya dawo falon tana yadda ya barta. Bai tsaya komai ba ya sunkuya zai ɗauke ta sai kawai ya ji bakinta cikin nashi tana mai kiss don haka ya biye mata yana maida mata martani abu kamar wasa sai ga Nusaiba ta haukace mai kamar wata zakanya sai hari take kawo mai ta ko'ina. Abin kuka ne ya samu mai kwarin ido, Jabeer shi kan shi yasan yana cikin jerin mazan farko a lamarin don haka sai Nusaiba ta tada tsohon zakin dake kwance yana jin yunwa.  Sosai suke yamutsa juna yadda ya kamata ganin abubuwan da take ya ji har a ransa wani ya riga shi amma sai ya danne kishinsa yasa a ransa ba haka bane ba kawai ta rasa budurcinta ne ta wani hanya ba wai ta hanyar ba wani ƙato ba.  Sun jima suna luguiguita junansu yadda ya kamata su duka kowa ya kai geji sannan Jabeer ya yi addu'ar saduwa da iyali ya shiga Nusaiba. Abin mamaki ya ba shi da ya ji ya kasa wucewa duk yadda ya so ya wuce lamarin ya faskara sai ya dawo hayyacinsa sosai domin kar da ya ja mata wahala saboda ya amince dai da gaske shi ne na farko da zai wuce gun. 
Ƙarshe dai sai da ƙyar ya samu ya wuce ta kuwa saka ihun gaske ta dawo hayyacinta ta kama kai ma shi duka ta ko'ina tana son ta ture shi amma ko gezau, shi a lokacin ma bai san inda kansa yake ba ita kaɗai ke a hayyacinta shi bai ma san duniyar da yake ciki ba. 
Sai da ya yi hani'an sannan ya mirgina gefe lokacin Nusaiba ko numfashi bata yi ta suma don azabar masifa. Da sauri ya ɗebo ruwa ya watsa mata, ta ja dogon numfashi sai kawai ta fashe da kuka tana kiran sunan Mama da Baba. Haka ya dinga lallaɓa ta har gari ya waye ya je ya haɗa ruwa masu zafin gaske ya ɗauke ta ya je ya saka ta ciki ta kuwa saka uban ihu tana cewa Allah Ya isa bata yafe ba mugu kawai da shi. Shi dai murmushi kawai yake ko ba komai Nusaiba ta biya shi tun da har ta kawo mai budurcinta gidansa to tabbas ba sauran wani zargi akan Nusaibar daga zuciyarsa kawai ya gane cewa Nusaiba irin mutanen nan ne masu nuna su ba su da kunya komai za su iya don kawai ace basu da kunya.
Haka ya dinga lallaɓa ta ya samu ya gama yi mata komai ya dawo da ita ɗaki ya bata magani ya je ya haɗa mata tea mai zafin gaske ya ji madara da Bournvita ya tada ta jikinta zafi rau ya ce ta sha tea yadda maganin zai mata amfani. 
Duk bakin Nusaiba sai ya koma tsit, ta kasa ko da musu tai ma Jabeer sai bin duk yadda ya yi da ita kawai take. A hankali ya janyo jikinsa ya mannata ya dinga shafa bayanta har barci ya sake kwashe ta. 
Godiya sosai yake ma Allah a ƙasan ransa. Nusaiba ta zo ma shi a cikakkiyar mace lallai mata halin su sai su.

Washegari tun da ya dawo sallar asuba bai kwanta ba zanin gadon ya ɗauka ya wanke shi fes dama tun cikin daren jiya ya shimfiɗa wani. Duk abin da yake tana kallonsa har a ranta ji take kamar ta kwarma ihu don masifar ɓacin rai amma ba dama,domin ta gefen zuciyarta tana jin wani abu mai kama da daɗi yana ratsa zuciyarta saboda yadda Jabeer ya dinga bi da ita ya yi mata daɗi sosai ya kuma tsaya mata a rai, tabbas ta sha wahala amma dai ta ji mugun daɗin yadda yake sarrafa jikinta kusurwa-kusurwa. Da ace tana son Jabeer tabbas da ta sha zumar ƙauna ba iyaka da shi a cikin gidan nan, amma matsalar guda ce bata shirya aure ba don haka ba za tai zaman aure ba duk daren daɗewa sai ya gaji da zaman jira ya sake ta. 
Jabeer har rana tai yana ta lallaɓa Nusaiba kowa ya zo ganin amarya sai ya koma da tsogumin angon nata lallaɓa amarya tana zumɓura baki wai ita ala dole don a gane an yi wani abin daren jiya.

Sai da yamma sannan jikinta ya yi ƙarfi da kanta tai wanka ta shirya cikin ƙananan kaya ta baje falo tana kallon India fuskarta tai wasai kamar wadda tai ciwo da gaske.


Washegari ne ta haɗu da su Ruky sun zo ganin ɗakin amarya tana ganinsu ta sakar masu fuska suka gaisa ba wadda ta sani a cikinsu yadda ta gansu fes komi ya ji ga wani uban ƙamshi da gayu duk sai ta ji ta raina kanta duk da take cikin mata masu mayyar tsabta kau. A nan ne take jin cewa wai sun zo wuce wa ne suka ji ana cewa an kawo amarya mai shegen kyau nan gidan sai suka biyo domin su gane ma idanunsu. Nan take Ruky ta amshi number Nusaiba tace ta bata account ta saka gudunmawar bikin ta bata sai ga manyan kuɗaɗe sun sauka daram a cikin account ɗin Nusaiba masu nauyi wanda nan take Nusaiba ta nemi diriricewa kan kuɗin. Ruky tai murmushi ta ja sauran suka fita tana ta ƙara kallon Nusaiba ƙarshe dai ta kasa haƙuri sai da ta ja Nusaiba a jikinta su kai hotuna. Sai taɓa Nusaibar take tana ƙara bayyana kyanta da taushin jikinta, har tai mata alƙawarin kawo mata sabulu da mayuka masu daɗi da gyaran fata idan za ta dawo.  Wannan ranar ba su kwana  sai da Ruky ta baza ma Nusaiba ruɗu sosai har ta sa ta fara jin zata amince da komi tace indai hakan zai sa ta zama gagara gasa a cikin tarin mata ta zama duk inda ta je sai an ganta an yi maganar ta. Wannan tunanin kai tsaye ta nemi shawarar Ruky abin da za tai ta zama kamar ita. Hakan ya yi ma Ruky daɗi don haka tace ta bari idan ta dawo daga ƙasar da za ta je zata dawo mata da cikar burinta. Tun daga nan kodayaushe suna cikin chat da Ruky a haka ta dinga tura mata number maza 'yan siyasa suna chat a haka kawai bata gansu ba kawai hotuna take tura masu amma kuɗaɗe suke tura mata masu nauyi. Sai dai ta kasa gane inda Ruky ta nufa na maganganun da take mata ga su nan dai su ba batsa ba su ba iskancin kai tsaye ba, ko kaya ta saka na barci sai Ruky ta turo mata hotonsu tace itama idan zata saka ta tura mata nata kayan barcin da saka ta gani. Tun tana jin ba daɗi lamarin har dai ta saba ita ta biye mata suna chat kamar wasu mace da namiji haka suke chat ɗin. Akwai ranar da Ruky ta kira ta bidiyo ta WhatsApp ta dinga yin wasu abubuwa sai da jikinta ya mutu, baki ɗaya ta ji komai ya kwance mata so kawai take ta je duniyar sama, shi kuma Jabeer tun wanda ya yi mata bai sake ba sai dai ya kwanta jikinta su kwanta tare kawai yana lallaɓa ta amma ba wani bayani daga nan, to yau duk yadda za ai sai dai a yi amma sai Jabeer ya cire mata sha'awar da Ruky ta sakar mata. A daddafe ta samu tai wanka tana jiran shi amma bai shigo ba don haka ta ɗaga waya ta kira shi. Ya yi mamakin ganin kiranta don haka cike da jin abin da ke faruwa ya amsa kiran. Sai dai kawai cewa tai ya zo gida tana son ganinsa ta kashe wayar ta.
Hankali a tashe ya shigo gidan amma abin mamaki tana kwance akan kujera ta caɓa kayan da kamar bata saka kaya a jikinta ba. Ya ɗauka ko bata lafiya amma yana taɓa jikinta domin ya ji ko da zafi sai kawai ta janyo shi baki ɗaya ta shiga sunsunar shi ta ko'ina tana sauke ajiyar zuciya. Nan take ya fahimci abin da ke faruwa dama daurewa kawai da tausanta ne kawai yasa yake ƙyale ta amma kullum cikin shan Lipton da lemun tsami yake saboda sha'awa. Bai jira komai ba ya amsa katin gayyatar tun yana lallaɓa ta har ya fahimci ita ma gwarzuwa ce a fagen don haka sai kawai ya saki jiki ya cigaba da aika mata da saƙon dake ƙara mata wutar lamarin kai tsaye. Tun daga lokacin ne Nusaiba ta dinga sakar ma Jabeer kaya yana ja lokaci zuwa lokaci saboda ita Ruky tana can ta waya take hura mata wutar ita kuma sai ta kira Jabeer duk inda yake ta baje mai komai ya kwasa tana jin tafi kowa samun gwarzon namiji mai ƙwazo a cin duniyar sama sanka-sanka haka kuma nau'i-nau'i mai gwanin garɗi. 

Lokacin da Ruky ta dawo ƙasar ne ta zo da kanta ta ɗauke ta duka je hotel tun Nusaiba na nuna bata san harkar lesbian ba har Ruky ta kai ta maƙura ta biye mata suka yi abin da suka so. Ruky ta ruɗe iya ruɗe wa jin yadda Nusaiba take cike kuma tinjim. Jikinta laushi ga taushi ga wani ƙamshi wanda bata san wane irin humra ko turare bane take amfani da su ba suna taimakawa wajen ƙara ma mutum shauƙi idan ya taɓa jikinta. A hankali Ruky ta maida Nusaiba cikakkiyar tantirar mace mai bin mata da maza, ta koya mata yadda yake bin bokaye da malamai. Tashin farko Kande ta fara neman shiga tsakaninsu tace bata yadda da Ruky ba dole Nusaiba ta fice daga sabgarta. Hakan yasa aka dinga samun saɓani da Nusaiba da uwarta Kande har sai da Nusaiba ta kai sunan Kande gun bokanta ya yi mata katanga da gidanta domin kodayaushe Kande na gidan Nusaiba tana hana ta rawar gaban hantsi sosai don haka tasa aka zaunar da ita waje guda aka mantar da ita ta taɓa haihuwar wata yarinya ma, ganin kamar sauran yayyenta da Baban za su kawo mata matsala su ma tasa aka shiga tsakaninta da su shi ne fa aka kafa mata dokokin da take jin yanzu sun yi mata tsauri bayan ta shafe shekaru biyar tana bin dokar yanzu ji take tamkar bata iya ci-gaba da bin dokokin musamman da aka ce za a ɗauke cikin jikinta. Tabbas ba zata bari a ɗauke mata ciki ba haka ba zata bari tai asarar duniyarta ba don haka dole akwai buƙatar ta sauya takunta kafin dare ya yi mata.


Ta ya kenan zata sauya takun nata jama'a?

Taku ce Haupha.