Zafin Soyayya Ya Sanya Wani Mutum Kone Gidan Su Budurwarsa

Zafin Soyayya Ya Sanya Wani Mutum Kone Gidan Su Budurwarsa

 

‘Yan sanda a jihar Ogun sun yi ram da wani mutum mai shekaru 43, Hassan Yusuf bisa zargin bankawa gidan su tsohuwar budurwarsa, Busayo Falola wuta saboda matsalar soyayya. 

An ruwaito cewa, wanda ake zargin ya kone gidan ne da ke lamba 127 a Old Scholar Palace da ke hanyar Igan a yankin Ago-Iwoye na karamar hukumar Ijebu ta Arewa a jihar. 
A cewar majiya, hakan ya faru ne bayan da budurwar tasa ta ki aurensa kana batun sulhu tsakaninsu ya ci tura, Punch ta ruwaito. 
Batun konewar na zuwa ne ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi a ranar Asabar cikin wata sanarwa. 
A cewar Oyeyemi, an kamo wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da wata mata mai shekaru 62 da aka ce itace mai gida, Adejoke Salau ta kai ofishin ‘yan sandan Iwoye. 
Kakakin na ‘yan sanda ya ce, mata mai gidan ta ce, jama’a sun ji hayaniya a gidan da misalin karfe 1:15 na dare, inda da aka duba aka ga gidan na ci da wuta, rahoton Vanguard. 
Ta kuma bayyana cewa, makwabta ne suka taimaka wajen shawo kan wutar tare da ceto masu hayan da ke ciki. 
Da aka je ofishin ‘yan sanda, budurwar ta ce ta ga tsohon saurayin nata a lokacin da haka ya faru.