Zaben Kananan Hukumomi: Gwamnan Gombe Ya Nuna Gamsuwarsa Da Tsarin Zabe

Zaben Kananan Hukumomi: Gwamnan Gombe Ya Nuna Gamsuwarsa Da Tsarin Zabe
 
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya bayyana gamsuwar sa na yadda Jama'a suka fito sosai suka kada kuri'a a zaben Kananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar.
 
Inuwa Yahaya, ya bayyana hakan ne Jim kadan bayan kada kuri'arsa da misalin karfe 11 na safiya a rumfar zaben sa ta AYU 010 da ke harabar Sakandaren kimiyya ta gwamnati da ke unguwar jekadafari a fadar jihar.
 
Yace fitowar Jama'ar bai ba shi mamaki ba domin hakan nada nasaba ne da irin ayyukan raya kasa da gwamnatin sa ke gudanarwa.
 
Gwamna Inuwa, ya Kuma ce akwai mataki na gaba na zuwa kotu dan neman hakki idan akwai wanda yake ganin bai gamsu da yadda aka gudanar da zaben ba.
 
Sannan sai ya yi kira ga Jama'a da cewa a taru a mara bayan ga duk Wanda yaci zabe domin samun damar ya iya sauke nauyin da aka daura masa.