Zababben Gwamnan Sokoto  Ya Bayyana Kudurori  9 Da Yake Son Cimmawa A Mulkinsa

Zababben Gwamnan Sokoto  Ya Bayyana Kudurori  9 Da Yake Son Cimmawa A Mulkinsa

 

Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto, zababben gwamnan jihar Sokoto ya bayyana kudurori  9 na gwamnatinsa, da kuma hanyoyin da zai bi don ciyar da jihar gaba. 

Ya bayyana wadannan manufofi ne a lokacin da yake yin taron manema labarai na farko a ranar Litinin a jihar ta Sokoto. 

Da yake bayyana manyan matsalolin da yake son magancewa, Aliyu ya yi alkarin inganta fannin ilimi, harkar lafiya da kuma samar da ruwan sha. 
Sauran abubuwan da ya ce zai maida hankali a kansu sun hada da noma, tsaro, karfafa matasa, inganta harkar kananan hukumomi waton ba su 'yancin cin gashin kai, taimakwa addini da tattalin arziki. 
“Gwamnatina za ta saurari koke da burin ‘yan jihar bisa hangen hanyar cimma alkawuran kamfen. 
“Zan karfafa aikin gwamnati ta hanyar yin gyara mai kyau, sannan na tabbatar da ana biyan albashi, fanso da giratuti a kan kari. 
"Gwamnati na za ta saurari suka da gyara mai ma'ana daga dukkan ‘yan Najeriya.” 
A bangare guda, ya bukaci abokan hamayyarsa da su yi hakuri, su zo a yi tafiya tare,  su dauki faduwarsu a matsayin kaddara kana su dafa masa don yiwa jihar hidima. 
"Ya bayyana godiyarsa ta musamman ga Sanata Aliyu Wamakko, ministan harkokin ‘yan sanda, Alhaji Maigari Dingyadi, shugaban APC na jihar, Alhaji Sadiq Achida da sauran manya da kananan magoya bayan APC.