Zababben Gwamnan Sakkwato Ya Yi Nadi Na Farko A Gwamnatinsa

Zababben Gwamnan Sakkwato Ya Yi Nadi Na Farko A Gwamnatinsa
 
Zababben gwamnan  Sakkwato Alhaji  Ahmad Aliyu Sokoto  ya aminta da nadin Malam Abubakar Bawa  a matsayin sakataren hulda da 'yan jarida a fadar gwamnatin jihar Sokoto.
 
Bayanin  na kunshe ne a wata takarda da  sakataren babban kwamitin karbar mulki na jamiyyar APC  Ibrahim Dadi Adare ya rattabawwa hannu.
 
Zababben gwamnan ya  taya murna ga sabon sakataren, ya kuma bukace shi da yayi amfani da kwarewar da yake da ita wajen ganin cewa an yayata shiraruwa da kuma tsare-tsaren gwamnati ga jama'ar jiha da wajenta.
Sanarwar ta ce wannan nadin dai ya soma nan take. Nadin da aka yi wanda shi ne na farko a gwamnatin da ake saran farwarta aranar Litinin mai zuwa.