Za'a Samu Sauyi a Kasafin Kudin Nijeriya Na Naira Tiriliyan 20 Da Gwamnatin Buhari Ta Ware a 2023?

Za'a Samu Sauyi a Kasafin Kudin Nijeriya Na Naira Tiriliyan 20 Da Gwamnatin Buhari Ta Ware a 2023?
 

Gwamnatin Najeriya Ta Ware Naira Triliyan 20 A Matsayin Kasafin Kudin Shekarar 2023:

 
Daga Abbakar Aleeyu Anache
 
Mahukunta a Najeriya sun ware Naira sama da Triliyan 20, a matsayin kasafin kudin shekara 2023: kuma shi ne kasafi mafi girma a tarihin kasar amma ma'aikatun da hukumomin gwamnati sun fara kokawa cewa kudaden da aka ware masu a kasafin kudin yayi masu kadan,
 
Ma'aikatu da hukumomi da dama da suka kara kasafin kudin su na shekara 2023 a gaban majalisar Dokokin kasar irin su ma'aikatar kula da tsaro da bayanan sirri da kuma ma'aikatar kula da harkokin kasashen waje da ma fadar shugaban kasa kanta sun koka cewa kasafin su na shekara 2023 yayi kadan, 
 
Shugaban kwamitin tsaro da bayanan sirri a majalisar Dattawa Abdullahi Ibrahim Danbaba yayi karin haske cewa barin ma'aikatu da hukumomin tsaron kasa babu isassun kudi ba abu ne da zai haifar da da mai ido ba, domin aiyukan tsaro na bukatan kudi musamman ma na samo bayanan sirri,
 
Danbaba ya ce majalisa za ta dauki matakin kawo wa ma'aikatun dauki ta yada doka ta tanada, 
 
A bangaren majalisar wakilai kuma takaddama ce ta kunno kai tsakanin kwamitin kula da ma'aikatar kasashen waje da Ministan ma'aikatan kasashen wajen inda shugaban kwamitin ya yi korafi cewa ma'aikatar ba ta bin ka 'idoji da aka shimfida mata ta yadda ake kashe kasafin kudi saboda haka majalisa ta hana a ba su kasafin kudin badi sai sun gyara, 
 
Shugaban kwamitin Yusuf Buba Yakubu ya yi baiyana cewa majalisa ta sha aikewa ma'aikatar takardar umurnin na gyara Ofisoshin jakadancin kasa a duk fadin duniya amma sai Ministan yayi burus da wasikun saboda haka majalisa ta dauki wannan mataki na dakatar da kasafin su na badi akan sai sun gyara,