Za mu shirya Rangadi Da 'Yan Jarida A Sakkwato Don Fito Da  Aiyukkan Tambuwal----Kwamishinan Yaɗa Labarai

Za mu shirya Rangadi Da 'Yan Jarida A Sakkwato Don Fito Da  Aiyukkan Tambuwal----Kwamishinan Yaɗa Labarai

 

Kwamishinan yaɗa labarai a Sakkwato Alhaji Aƙibu Ɗalhatu ya bayyana cewa zai haɗa hannu da 'yan jarida da ke aiki a jihar don ƙara fito da aiyukkan da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi wa al'ummarsa.

Kwamishinan ya yi wannan kalami ne a lokacin da 'yan jarida masu aika rahoto a waje suka ziyarce shi  a ofishinsa a wanan Alhamis ya ce za su shirya rangadi da 'yan jarida a Sakkwato don bayyana aiyukkan Tambuwal.
Akibu ya ce gwamnatin Tambuwal ta gudanar da dimbin aiyukkan cigaban jiha da suke abin alfahari ga al'umma don haka za a zakulo su don tabbatar da maganarsa.
Ya nemi mutanen da ke yada kalamai na karya kan gwamnati da gwamna Tambuwal da su ji tsoron Allah su daina domin wannan hakan ba zai haifa masu Da mai ido ba.
Da farko shugaban kungiyar Malam Habibu Harisu ya sanarda kwamishinan sun kawo ziyara ne domin taya shi murna kama aiki, da samun fahimtar juna domin aikinsu ya zama mai inganci da karbuwa a cikin al'umma.
Harisu ya bayyana cewa su manema labarai abokan kowa ne da son cigaban jiha, ba su da wasu mutane da suka ware don yi masu aiki fatar da suke da ita cigaban Sakkwato da Nijeriya baki daya.