Daga Abdullahi Alhassan, Kaduna
Tsohon shugaban kungiyar Al'ummar kudancin Kaduna, wan da yanzu shine Dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar Leba wato (Labour party)Mista Jonathan Asake ya bayyana cewa tsaro shine abinda zai maida hankali wajen ganin ya shawo matsalar al’amarin na farko da zai dauki mataki a kansa, ldan jama’a suka zabe shi a matsayin Gwamnan Jihar Kaduna a zaben 2023 mai zuwa.
Mista Asake ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna sa’ilin da ya ziyarci cibiyar yan jarida ta kasa NUJ reshen Jihar kadunan.
Tsohon shugaban kungiyar Al'ummar kudancin Kaduna,Jonathan Asake ya ce "a halin da ake ciki Manoma ba su iya zuwa Gonakinsu saboda matsalar tsaron da ake fama da ita wanda hakan ya maida harkar Noma baya da kuma keda mutukar matsala don samar da abinci.
Ya kuma kara da cewar “Akwai wasu makarantu da dama da duk sun kulle a halin yanzu sakamakon matsalar tsaron da ake fama da ita,haka kuma akwai wasu kamfanoni a Jihar Kaduna da suka kwashe kayansu daga cikin Jihar suka koma wata Jiha domin matsalar da ake da lta ta tsaro, da akwai wasu kuma masu kokarin zuba karin da suka kasa yin katabus wanda sakamakon hakan duk sun canza Jiha.
Gubu da kari "Masu Garkuwa da satar jama’a duk suna neman mamaye ko’ina, idan kuma sun kama mutane sai su bukaci wasu kayayyaki kamar Babura, kudi da wasu kayayyaki,kai har cewa jama’a suke aje wuri kaza inda ake sayar da Baburan aje wurin wane domin za su gaya maka sunan mai sayar da Baburan da farashin da ake Sayarwa kuma idan an je wurin hakan za a gani,
Amma magana a nan ta yaya aka kasa yin maganin wadannan mutane, don haka idan na zama Gwamnan Jihar Kaduna zan tabbatar da yin maganin matsalar tsaro”, inji Asake.
“Ba za mu zauna kawai muna cin bashi ba, idan mun lashe zabe domin bashin da ake ci masu zuwa nan gaba ba za su iya biya ba” don haka idan an zabe ni na lashi takobin zan kirkiri hanyoyin samun kudin shigar da Gwamnati za ta yi dogaro da su.
Zamu canza lamarin tafiyar da Gwamnati saboda mu za mu ta fi da kowa ba wani bambanci ko kadan.haka kuma zan habbaka rayuwar Matasa da Mata.
"Domin a yanzu halin da ake ciki matasa na ganin akwai matsala a tattare da gudanar da rayuwarsu nan gaba don haka a shirye suke su tabbatar sun kwato yancinsu a ko’ina suka kasance.
Hakazalika “Muhimmin lamari ne za mu inganta rayuwar matasa da mata, kuma za mu yi wani abu domin ta yaya za a Sanya harkar ilimin mata cikin wani yanayi har a Jihar Kaduna ake biyar kashi dari uku na karatun makarantar jami’a.
Yace zai bunkasa fanin Noma kunga Saminaka,data kasance wurin da ke Noman Masara da ya fi na ko’ina a fadin Afrika ta Yamma,da kuma Noman Citta da ake yi tun daga Kachia ,wanda har tsohon Gwamnan Kaduna Marigayi Balarabe Abdulkadir Musa ya gina kamfanin sarrafa Citta, amma a yanzu wane hali suke ciki?
Mista Asake ya kara da cewar a bangaren kiwon lafiya, mazabu 255 muna da wuraren kula da kiwon lafiya da a yanzu kawai sun tsaya ne a kan suna kawai domin yanayin da suke ciki abin tausayi ne, don haka za mu tabbatar da yin gyara na musamman domin jama’a su samu kulawa na musamman a kiwon lafiyar.