Zaɓen 2023: Hon. Kaitafi Ya Nemi Cikakken Goyon Bayan Al'ummar Bade/ Jakusko

Zaɓen 2023: Hon. Kaitafi Ya Nemi Cikakken Goyon Bayan Al'ummar Bade/ Jakusko

Daga Muhammad Maitela, Damaturu.

Dan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya don wakiltar kananan hukumomin Bade da Jakusko a jihar Yobe, a zaben 2023 mai zuwa, Hon. Sani Ahmed Kaitafi ya nemi goyon bayan al'ummar yankin tare da addu'o'i kan wannan manufa, musamman masu ruwa da tsaki a harkar zabe domin samun nasara tare da sauke nauyin da jama'a suka dora masa na kiransa ya tsaya takarar, baya ga saya masa fam, inda ya jaddada cewa wannan babban kalubale ne wanda yake bukatar goyon baya da addu'a. 

Hon. Kaitafi ya bayyana hakan ne a sa'ilin da yake yi wa cincirindon dubban jama'ar yankin suka tarbe shi domin ya gabatar da kansa ga shugabanin jam'iyyar APC a matakin unguwa, gunduma da karamar hukuma bisa aniyarsa ta tsaya wa takarar; kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tanada, wanda ya gudana da ranar Asabar a garin Gashuwa, shalkwatar karamar hukumar Bade. 

Daraktan yakin neman zaben dan takarar- Mallam Bukar Dala shu ne ya gabatar da Hon. Sani Kaitafi ga shugaban jam'iyyar APC na gundumar Katuzu, Mallam Husaini Kachalla Yagara wanda ya bayyana gamsuwarsu da matakin da dan takarar ya bi wanda ya ce haka tsarin jam'iyyar ya tanada, inda ya yi masa fatan alheri. Kana kuma, shugaban jam'iyyar APC na Katuzu ya jagoranci tawagar dan takarar zuwa ga shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Bade, Alhaji Bukardima Lawan. 

A jawabin shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Bade, ya ce, "Yau 7/5/2022 Sani Ahmed Kaitafi ya zo gaban shugabanin jam'iyyar APC na karamar hukumar Bade domin ya gabatar da kansa, ta hannun shugaban jam'iyyar APC da mukarabbansa na gundumar Katuzu tare da rakiyar dattawa hadi da daimbin magoya bayan sa, domin mika takardarsa ta neman tsayawa takara a jam'iyyar APC, wanda kuma mun karbe shi hannu biyu. Saboda haka, Sani Kaitafi ya na daga cikin yan takarar da suka nuna sha'awar takara kuma wannan shi ne abin da jam'iyya take bukata, haka yan jam'iyya tare da shugabancinta haka yake bukata daga kowane dan takara- mutuntawa da karramawa."

"Saboda haka mun shaida Sani Ahmed Kaitafi ya nuna sha'awar takarar kujerar majalisar wakilai don wakiltar Bade/Jakusko a zaben 2023 mai zuwa. Kuma muna add'ar Allah ya bai wa mai rabo sa'a tare da hakuri idan an samu akasin hakan, kuma shima da kansa ya nuna wannan. Kuma a jam'iyyance muna yi masa fatan alheri tare da sanar da cewa shi ne dan takarar farko wanda ya gabatar da kansa ga jam'iyyar APC a wannan yankin." In ji shugaban jam'iyyar APC.

Dandazon dubban jama'a ne suka tarbo Sani Ahmed Kaitafi inda ya fara da kai gaisuwar girmamawa ga Sarkin Bade, Mai Alhaji Abubakar Umar Suleiman a fadarsa, inda daga bisani ya gana da shugabannin jam'iyyar APC, dattawa da yan uwansa a Katuzu, yayin da ya nemi goyon bayan su tare da addu'o'in samun nasara bisa wannan kuduri nashi.

Ya ce, "Na zo ne nan don na gabatar da kaina tare da neman goyon bayanaku ku bani dama don na wakilici wadannan kananan hukumomi na Bade da Jakusko a zauren majalisar wakilai ta tarayya dake Abuja. Sannan kuma muna neman wannan wakilcin ne ba don kanmu ba face kawai domin kawowa jama'armu ci gaba wanda ba lalle ne sun san dashi ba; ma'ana zamu shiga lungu da sako ne wajen ganin mun kawo gagarumin ci gaba a wannan yanki."

"Har wala yau, ina neman albarkar ku a zamanku na iyaye, saboda addu'arku daya tana da muhimmancin gaske a kaina fiye da ta kowane mutum a matsayinku na mahaifana, bisa ga wannan don Allah da Annabinsa (SAW) ku yi min addu'a kuma ku sanyawa wannan manufata albarka. Haka kuma ina so nayi amfani da wannan dama na nemi alfarma ta hannunku wajen mika sakona na gaisuwa ta musamman ga babana Sanata Ahmed Ibrahim Lawan, wanda shi ne ya reneni har na kawo wannan matsayi a siyasance tare da bani damammaki daban-daban wadanda suka taimaki rayuwata. Saboda shi kansa Sanata Ahmed Lawan bashi da wakilan da suka wuceku. Ina neman alfarmarku ku isar masa da sakon godiyata Allah ya saka mishi da alheri."

Hon. Kaitafi ya bayyana cewa, "Makasudin wannan taro a yau shi ne domin gabatar da kaina ga shugabanin jam'iyyar APC dangane da aniyata ta tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai a Bade/Jakusko a zaben 2023 mai zuwa. Kuma mun yi haka ne saboda haka tsarin jam'iyyar APC ya tanada, kuma na mika takardata ta tsayawa takara tare da amincewa dani. Sannan nayi imanin cewa babu wani dan takarar da ya kaini cancanta, kuma na sani zan yi abin da mafi yawa ba zasu iya ba. Kuma wannan ba domin Allah yafi sona ba face kawai ilimin da Allah ya bamu tare da sanin makama bakin gwargwado saboda mun dade da sanin ciki da wajen majalisar kuma mun san Abuja da duk inda ya dace mu kutsa kai wajen nema wa al'ummar yankin mu ci gaba." 

"Kuma ko shakka babu na san jama'a da dama suna kyautata zaton zan kawo musu ci gaba mai ma'ana a wakiltarsu da zan yi, kuma duk da yake mun dade a harkokin siyasa amma jama'a sun nuna min tsantsar kauna. Sannan kuma ina rokonsu don Allah a ci gaba da yi mana addu'a tare da goyon baya. Kuma in sha Allah zan yi kokari wajen samar da ayyukan yi tare da tallafa wa jama'a wajen samun rayuwa mai inganci. Kuma zan mayar da karfi sosai wajen samar da tallafin da zai bunkasa ayyukan noma a wannan yanki namu.". In ji Kaitafi.