Home Siyasa Yayin da Nijeriya ke cikin ƙunci, Shugaba Tinubu ya tafi hutu a...

Yayin da Nijeriya ke cikin ƙunci, Shugaba Tinubu ya tafi hutu a Turai — Atiku Abubakar

7
0

Ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya soki tafiyar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi zuwa nahiyar Turai domin hutu na tsawon makwanni uku, yana mai bayyana matakin a matsayin rashin kyakkyawan shugabanci a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsanancin halin ƙunci da rashin tsaro.

Atiku ya bayyana haka ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada cewa yayin da miliyoyin ‘yan Nijeriya ke tsaka da fama da matsin rayuwa ta yadda ba sa iya yin tafiya, shugabansu kuwa yana can yana shawagi a sararin samaniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here